Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Inter Milan na zawarcin Antonio Conte

Kulob din kwallon kafa na Inter Milan da ke wasa a gasar rukuni-rukuni na Serie A na kasar Italiya ya fara zawarcin tsohon kocin Chelsea Antonio Conte.

Kulob din ya sanar da haka ne a ranar Litinin da ta wuce jim kadan da rabuwa da kocinsa Luciano Spalletti da ya kasa tabuka abin kirki a kakar wasa ta bana.

ADVERTISEMENT

Antonio Conte wanda ya yi ban kwana da kulob din Chelsea a kakar wasan da ta wuce, shi ya bullo da dabarar yin wasa ta 3-5-3 a kulob din Chelsea wadda hakan ta sa ya samu nasarar lashe Kofin Firimiya da na kalubale (FA) a shekararsa ta farko.

Sai dai daga baya ya samu sabani da wadansu daga cikin ’yan kwallon kulob din da hakan ta sa ya bar kulob din babu shiri ganin yadda kulob din ya shiga matsala a kakar wasan da ta wuce.

ADVERTISEMENT

Kulob din Inter Milan ya yi ban kwana da gasar Zakarun Turai inda yanzu ya koma zai fafata a gasar Europa da za a ci gaba da yi a watan Fabrairun 2019.

Ana sa ran nan gaba kadan  Inter zai kulla yarjejeniya da Conte idan ya amince da tayin da aka yi masa na horar da kulob din.