✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ba za ta sarayar da hakkin nukiliyarta ba – Rowhani

Shugaban Iran Hassan Rowhani ya bayyana aniyar kasarsa ta tattaunawar gar- da-gar da Amurka kan shirinta na nukiliya, don a cewarsa kiran da Amurka ta…

Shugaba Hassan Rowhani na IranShugaban Iran Hassan Rowhani ya bayyana aniyar kasarsa ta tattaunawar gar- da-gar da Amurka kan shirinta na nukiliya, don a cewarsa kiran da Amurka ta yi na kakaba musu takunkumi rashin fahimta ne.
Da yake jawabi a wajen taron ’yan jarida, alokacin da ya kama ragamar mulki, Rowhani ya ce ba zai sarayar da ’yancin Iran ba, amma yana kokarin tabbatar wa kasashen Turai cewa babu wani abin tsoro a tattare da shirin: “A matsayina na Shugaban kasar Jamhuriyar Musulunci, ina sanar da cewa akwai kokarin da ake yi na warware wannan matsala, sannan za mu la’akari da abin da ke damun daya bangaren,” inji shi.
Rowhani shi ne jagaba wajen sasanta matsalar kasar da Turai kan shirin nukiliya, a  lokacin mulkin Shugaba Mohammad Khatami. Tsattsauran ra’ayin magabacinsa, Muhammad Ahmadinejad ya haifar wa kasar takunkumi daga Tarayyar Turai da Amurka, inda aka tunkari man Iran da harkokin bankinta. Don haka sabon shugaba ya kuduri aniyar shawo kan wannan matsala da ta addabi kasarsa.