✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta nemi sulhu da makwabtanta

Kasar Iran ta sake jaddada aniyarta na neman shirya tattaunawar zaman lafiya tsakaninta da makwabtan kasashen yankin, wato Turkiyya da kuma Syria. Ministan Harkokin Wajen…

Kasar Iran ta sake jaddada aniyarta na neman shirya tattaunawar zaman lafiya tsakaninta da makwabtan kasashen yankin, wato Turkiyya da kuma Syria.

Ministan Harkokin Wajen Kasar,  Javad Zarif ne ya sanar da hakan, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, yau Litinin.

Mista Zarif , ya bayyana cewa bazuwar wutar zaman tankiya a yankin na faranta ran ‘yan ta’adda da kuma masu tallafa musu ne kawai.

“Kauce wa zubar da jini tare da mutunta diyaunci da kuma iyakokin kowace kasa nada matukar muhimmanci a gare mu,” inji Mista Javad Zarif.