✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta yi watsi da bukatar ganawa da Amurka bayan korar John Bolton

Sa’o’i kadan bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tube John Bolton mai ba shi shawara kan sha’anin tsaro daga mukaminsa, Mista Trump…

Sa’o’i kadan bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tube John Bolton mai ba shi shawara kan sha’anin tsaro daga mukaminsa, Mista Trump ya ce a shirye ya ke ya gana da Shugaban Iran Hassan Rouhani ba tare da wani sharadi ba. Sai dai kasar Iran ta yi watsi da bukatar Amurka na ganawa a tsakanin Shugaba Trump da Rouhani a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya da zai gudana a wannan wata a birnin New York.

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya Majid Takht-Rabanchi ya ce Rouhani zai gana da Trump ne kawai idan Amurka ta kawo karshen ta’addancin kasuwancin da take yi wa kasarsa, wajen cire mata takunkumi.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo da Sakataren Baitulmali Steben Mnuchin su ne suka ce a shirye Shugaba Trump yake ya gana da Shugaba Rouhani ba tare da gindaya sharudda ba, bayan ya kori mai ba shi shawara kan harkokin tsaro John Bolton. A watan jiya, Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ke shiga tsakanin kasashen biyu, ya bayyana cewa akwai yiwuwar ganawa a tsakanin bangarorin biyu.