✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta zargi Saudiyya da hannu a zanga-zangar kasarta

Shugaban Rundunar ’Yan sandan sashin addini da siyasa na Iran, Ali Riza Edyani ya bayyana cewa Saudiyya na goyon bayan masu zanga-zangar adawa da karin…

Shugaban Rundunar ’Yan sandan sashin addini da siyasa na Iran, Ali Riza Edyani ya bayyana cewa Saudiyya na goyon bayan masu zanga-zangar adawa da karin farashin man fetur a kasar Iran din.

Edyani ya ce “A lokacin da ake tuhumar mutanen da aka kama, an gano wadansunsu na da alaka da Saudiyya, wadansu kuma Kungiyar Mujahideen da kuma magoya bayan Shah. An tuhumi mutum 182 da zama manyan makiyan Iran.”

Edyani ya ce wani yaki ne ya barke tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar kuma manufar makiyan kasarsu ita ce su mayar da Iran ta zama kamar Iraki da Siriya.

Al’ummar Iran da suka sake fada wa mummunan yanayin tattalin arziki sakamakon takunkumin da Amurka ta saka musu, sun fara zanga-zangar adawa da ninka farashin man fetur har sau uku da aka yi a kasar a ranar 15 ga watan Nuwamban nan.

Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce akalla mutum 115 aka kashe sakamakon zanga-zangar.

Jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei ya goyi bayan matakin gwamnatin kasar na kara farashin man fetur da ta yi.

Ya zargi batagari da lalata kayayyaki a zanga-zangar, wacce ta yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum biyu. Kalaman nasa sun zo ne a daidai lokacin da gwamnatin ta rufe Intanet a duk fadin kasar Iran a kokarin dakile zanga-zanga kan karin farashin man da gwamnatin ta yi da kashi 50 bisa 100.