✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Irin canjin da Buhari zai kawo idan ya koma mulki

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa muddin Allah Ya sa ya samu nasara a zaben badi, ya kuma samu ikon kammala wa’adinsa na…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa muddin Allah Ya sa ya samu nasara a zaben badi, ya kuma samu ikon kammala wa’adinsa na biyu, to da yardar Allah za a ga irin salon mulkin da zai yi da kum abin da zai bari bayan ya kammala. Shugaban ya yi ikirarin haka ne a lokacin da yake ganawa da wasu daga cikin masana a kan fannoni dabam-daban na rayuwa `yan asalin kasar nan mazaun kasashen Amurka da Kanada a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 73, da aka kammala a birnin New York na kasar Amurka.

Shugaba Buhari, wanda ya nuna matukar damuwarsa a kan irin yadda `yan Bokon suka yi gum a lokacin mulkin jam`iyyar PDP, na tsawon shekara 16, inda jam`iyyar ta yi kaca-kaca da tattalin arzikin kasar nan. Yana mai cewa “Ba su ce komai ba a lokacin ayyukan Hukumar Kula da Asusun Rarar Mai wato PTF, da muka gina hanyoyi daga Ikko zuwa Abuja, da Anacha zuwa Fatakwal. Tun daga wancan lokaci na 1999 zuwa 2015, ba a kara kula da hanyoyin kasar nan ba. A shekarar 1983, manyan hafsoshin sojoji sun taru, sun dora ni a karagar mulkin kasar nan, lokacin da na tattara `yan siyasa na daure su, na fada masu suna da laifi, har sai sun tabbatar da akasin hakan. Muka kwace dukiyoyi da kaddarorin da suka sata. Amma daga bisani ni kaina aka tsare ni, aka kuma mayarwa da `yan siyasar dukiyoyi da kaddarorin da suka  handame.” In ji shugaba Buhari ta bakin mai magana da yawunsa Mista Femi Adesina.

Wani batu da shugaba Buhari ya tabo a ya yin ganawar shi ne irin yadda ya yi ta tsayawa takarar shugabancin kasar nan har sau uku, sai a na hudu Allah Ya ba shi nasara abin da ya ce a duk tsawon wancan lokaci ana ta zirga-zirga zuwa kotu, ba tare da samun nasara ba, amma kuma “ina cewa Allah na nan”. Yana mai la`akari da cewa talakawan kasar nan kadai suka kula da irin halin da nake ciki, don haka, hatta mata masu ciki, suna kan layin zabe suna nakuda, sai su koma gida su haihu, sannan su dawo su bi layi su kada mani kuri`a. Ni ma yanzu su ne gabana na yadda zan inganta rayuwarsu.

A lokacin da yake karin haske kan bukatar `yan kasar nan da suke zaune a kasashen na Amurka da Kanada su dawo gida don bada ta su gudummuwar wajen gina kasar nan, shugaba Buhari ya shawarce su da in har za su bada gudummuwa, to, su bayar a kan fannin ilimi a yankunansu. Yana mai jaddada cewa muddin jama`a suka ilimanta, to kuwa ba za su rika zuba ido a kan irin sakarcin da masu mulki suke musu ba. Ya kuma bada tabbacin cewa yana kan iyakacin kokarinsa na cika alkawurran da ya dauka na magance matsalolin tsaro da farfado da tattalin arzikin kasar nan da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Babu shakka irin matakan da shugaban Buhari zai ci gaba da dauka idan Allah Ya ba shi nasara a zaben na badi, har ya samu kammala wani zangon na shekara hudu, su ne manya-manyar fargaban da masu adawa da gwamnatinsa da ma na cikinta masu guntun kashi a gindi suke jin tsoron muddin shugaba Buharin ya yi nasara a zaben na 2019, za su fuskanta, shi ya sanya a cikin wannan shekarar jajibirin zaben za su yi dukkan irin kulumbotan da za su iya don tabbatar da cewa shugaba Bahuri bai kai ga nasara.

Alal misali, a cikin kusan shekara hudu da hawan gwamnatin Muhammadu Buhari, zuwa yanzu ta yi nasarar kusan kawo karshen tada kayar bayan `yan kungiyar Boko Haram da ake fama da rikicinsu yau kusan shekara goma. Kasancewar Gwamnatin Tarayya a lokacin PDP, a karkashin jagorancin tsohon Shugaban Kasa Dokta Goodluck Jonathan ba ta mayar da hankalin da ya kamata ba wajen yaki da `yan kungiyarta Boko Haram. Kamar ma yadda ta bayyana yanzu a duniya, gwamnatin ta Jonatahan ita ta rika raba makudan biliyoyin Nairorin da ta yi wa duniya ikirarin ta ware don sawo makaman da za ta yaki `yan kungiyar Boko Haram da sauran masu ta`addanci, amma ta buge da raba su ga magoya baya da abokai da aminai da sunan yadda shugaba Jonatahan zai kai ga nasara a zaben 2015.

Idan mai karatu kuma ya yi la`akari da yadda gwamnatin Buharin ta mayar da hankali a kan yaki da cin hanci da rashawa, annobar da aka yi  ittifakin cewa ita ce ummulhabasin dukkan wani rashin samun ci gaban da kasar nan ta shiga, zai ga cewa kafin zuwanta akwai gwamnonin jihohi zubin farko wato tsakanin 1999 zuwa 2007, da wasu makarrabansu da Hukumar EFCC, ta kai kotu, tun bayan saukarsu, amma ake ta kongaba-konbaya, akan shari`unsu, sai a zuwan wannan gwamnati kuma a cikin `yan watannin da suka gabata aka samu daure biyu daga cikin tsofafffin gwamnonin, wato na Jihar Taraba Rebaran Jolly Nyame da Jihar Filato Sanata Joshua Dariye, duk kuwa da zargin da ake ma gwamnatin ta Buhari akan yaki da cin hanci da rashawar na ta ba ya mayar da hankali akan tsofaffin `yan jam`iyyar PDP da suka yi kaura su komo jam`iyyar ta APC, tun farkon kafuwarta a shekarar 2014.

Amma nakan ce da masu wancan zargi, su yi hakuri kuma su yi fatan Allah Ya sa shugaba Buhari ya yi nasarar samun wa`adi na biyu, su ga irin yadda gwamnatinsa za ta karke da irin wadancan macuta, mayaudara kuma mugaye, da suka dade suna tsotse jinin talakan kasar nan, ta hanyar sace dukiyoyinsu. Buharin ya ce “Shi na kowa ne, amma kuma ba na kowa ba” a ranar 29-05-15 a lokacin rantsar da shi. Me jama`ar kasar nan suke ci, na baka na zuba? Ya gama mulkinsa ne bai kai ga makarraban nasa ba? Duk mai fatan a gyara kasar nan rayuwa ta inganta gwargwadon zarafi, to ya kamata ya dukufa da addu`o`in Allah Ya ba `yan kasa ikon zaben dukkan mutamin da suka yi yakini na gari ne da zai bada gudummuwar da za ta kawo yadda za a gyara kasar nan.