✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Irin wakokin da ba zan yi ba ko za a ba ni Naira tiriliyan dubu – Sardaunan Mawaka

Fitaccen mawakin fadakarwa da kuma nishadi, Abdul’aziz Dahiru wanda aka fi sani da Sardaunan Mawaka ya ce ko za a ba shi Naira tiriliyan dubu,…

Fitaccen mawakin fadakarwa da kuma nishadi, Abdul’aziz Dahiru wanda aka fi sani da Sardaunan Mawaka ya ce ko za a ba shi Naira tiriliyan dubu, ba zai yi wakokin batsa da na cin mutunci ba.

Mawakin ya ce abin bakin ciki ne irin yadda mawakan yanzu suka fi mayar da hankali kan wakokin cin mutunci da batsa maimakon na fadakarwa da nishadantarwa.

Ya ce, “Zan yi kowace irin waka amma ban da wakoki iri biyu, wakokin da ba zan yi a rayuwata ba sun hada da wakar batsa, ko kuma a sa ni in ci mutuncin wani dan siyasa ko wani mutum mai mutunci.”

Sardaunan Mawaka ya kara da cewa babu abin da ke lalata mawaki, ya karya masa daraja kamar a sa shi ya ci mutuncin wani,

Ya ce, “Saboda duk wanda ya sa ka ci mutuncin wani, to daga ranar ya gama da kai, kuma zai rika kallonka a matsayin sakarai, domin ya san ba ka da amana kuma ba ka da tabbas, saboda ya ba ka kudi ka zagi wani, to shi ma bai wuce a ba ka kudi ka zage shi wata rana ba.”

Mawakin ya nanata cewa wakokin batsa kuma suna karya mutuncin mawaki a idon jamaa, domin kowa zai rika kallon mawaki a matsayin mara tarbiyya da daraja.

“Mawakin da ke wakokin batsa zai zama mara kima, domin babu mutumin kirkin da zai yabe shi, sannan inda babbar matsalar take shi kansa da ke yin wakar batsar ba zai so in ya mutu a kunna wakokinsa ba, tunda ya san ba karatun Kur’ani ba ne ba kuma wa’azi ya yi a lokacin da yake raye ba,” inji shi.

Mawakin ya shawarci mawaka su fahimci cewa waka wata baiwa ce daga Allah, “Mai yin waka zai iya mika sako ga al’umma ya kuma isa kai-tsaye, sannan a amfana, don haka kada mawaki ya yi amfani da wannan baiwar wajen gurbata tarbiyya ko cin mutuncin wani,” inji shi.

Ya ce, “Ya kamata mu ji tsoron Allah a duk al’amuran rayuwa, duk abin da za mu yi mu tsaya mu auna cewa idan mun yi, to mene ne amfaninsa ko rashin amfaninsa. Saboda ko mawaki bai kiyaye don kansa ba, to ya kiyaye don zuriyarsa, domin ba zai so ’ya’yansa su ji cewa shi ne ya yi wakokin banza ko masu gurbata tarbiyya ba.