✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ishara Ga Mata: Ta yaya tsiraici zai zama kwalliya?

Ya ku masu bibiyar lambun FDK, a wannan farfajiya ta Dausayin Kauna. Yau fa abin ya kabura, ya girmama, don haka kada ku ga laifina…

Ya ku masu bibiyar lambun FDK, a wannan farfajiya ta Dausayin Kauna. Yau fa abin ya kabura, ya girmama, don haka kada ku ga laifina a wannan tsokacin da zan yi. Abin ne na ga yana neman wuce makadi da rawa, inji masu iya magana. Yau haka ne mana, domin kuwa tun muna jin labarin daga nesa, a hankali ya gangaro kasarmu, sannu-sannu har ya dan matso gefenmu. Tun muna kallonsa a gefenmu muna mamaki, muna kushewa da yin dariya, sai ga shi a yau ya shigo cikinmu tsundum. Ba ma shigowa kadai ya yi ba, har ma ta kai ga da hannuwanmu muke sanya dukiyarmu mu saya kuma mu rika yin takama a cikin ’yan uwa da dangi.

“Haba FDK, sai zuba kake ratata kamar burmammen bokiti. Yaya za ka yi ta surutu alhali ba ka gaya mana abin da kake wa kwarmato ba?”

Abin da wani zai ce ke nan, musamman ganin na bude bayanina a lullube. Ni kuwa na ce ku kara hakuri, abin ne kawai yake ci mani rai kuma yake dugunzuma mani tunani. Na lura da yadda muke sayar da mutunci muna sayo rashin mutunci muna daurawa. Ina mamakin yadda muke jefar da kyakkyawa, muna sayo mummuna muna kakaba wa kanmu. Ga shi kuma muna jefar da kunya muna sayo rashin kunya muna kakaba wa kanmu.

“Ni dai na fara gajiya da wannan surutan naka FDK,” inji wata da take ta shirin jin inda na nufa. “Kawai mu ka fito fili ka bayyana mana abin da kake son fada.”

Haba malama, ki dan kara hakuri mana, zan kawo har inda nake son kawowa kuma za ki fahimta da irin bakin cikin da nake ciki. Idan na zo kan batun nawa, lallai za ki gane cewa lallai dole ne in yi sharar hanya da nuna mamaki har ma da jimami kafin in kai ga batun nawa.

“To muna jin ka, bari mu kara kasa hajar zomo, don sauraren ka.”

Yauwa, to ina son yin magana ne yadda matanmu suke wata irin kwalliya, yadda suke saka kayan tsiraici wai da sunan wayewa.

A wannan zamanin, za ka ga yarinya ta sanya sutura amma rabin nononta a waje, rabin gadon bayanta a waje. Za ka ga ta saka matsattsun kaya, masu nuna dukkan surar jikinta. Kuma wai wannan duk matan suna yi ne da sunan wayewa. Ni kuwa na ce to ina hankalinmu yake?

Abin da irin wadannan matan ba su gane ba shi ne, maimakon burgewa, suna kaskantar da kansu ne. Idan suna yi ne domin jawo hankalin maza domin su kaunace su, to su sani babu wata kauna ta gaskiya da namiji zai miki bayan ya gama ganin sirrin jikinki. Idan kina son hujja saurara ki ji.

Duk wani abu mai daraja, boye shi ake yi ’yar uwa. Mu dauki misali da kudi ko gwal ko wata dukiya da muka mallaka, ai boye su muke yi a wuri mai kyau da tsaro mai inganci.

Mu kara daukar misali da abinci ko wani abin kwalam da makulashe. Misali, a ce ka kirawo mutum biyu masu sayar da abinci domin ka saya. Daya sai ya zo da abincin a rufe, daya kuma ya zo da nasa tunya-binya a bude, duk iska ta buge shi; don Allah abincin wa za ka saya cikin biyun nan? Za ka saya daga hannun wanda ya bar nasa a bude ne ko kuwa wanda ya rufe shi ruf?

Idan mace ta sanya wadatattar sutura da ta rufe mata dukkan jikinta da tsiraicinta. Babu shakka ta yi wa kanta kariya ne kuma ta rufa wa kanta asiri. Abin nan da kike boyewa, shi ne namiji yake son gani idan ya biya sadaki an daura maku aure. to ke kuma sai kika sake shi a titi kowa yana gani, to me kuma ya rage?

Mu dauki misali da wani kunkuru, wanda ya ce shi ya gaji da zama cikin koko. Don haka sai ya sanya duk aka sassake masa kokon nan daga jikinsa, ya fito jikinsa subul – tinya-binya!

Bayan kunkurun nan ya samu kimanin minti talatin a waje, iskar duniya ta bice shi sai ya ji gaba daya jikinsa ya canja, fatar jikinsa ta yamushe. Nan da nan cinnaka ya samu galaba a kansa. Bai ankara ba sai ya samu kansa yana ta mirgina-mirgina saboda azabar da yake sha a sanadiyyar rashin kokonsa. Daga lokacin nan ya gane cewa ashe kokon nan da Allah Ya halitta masa kamar sutura ce gare shi kuma garkuwa ce mai amfani ga jikinsa.

Don haka, ya ku mata masu shigar tsiraici, ku dauki izina daga kunkurun nan, domin kuwa sutura garkuwa ce a gare ku, rufin asisri ce.