✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iska mai tsananin sanyi ta mamayi Amurka

Wata iska mai tsananin sanyi ta mamatye tsakiyar Amurka, inda yanayin sanyin ya rubanya wadanda aka yi a shekaru 20 da suka gabasta, al’amarin da…

Wata iska mai tsananin sanyi ta mamatye tsakiyar Amurka, inda yanayin sanyin ya rubanya wadanda aka yi a shekaru 20 da suka gabasta, al’amarin da ya kai ga an samu asarar rayuka hudu, an kulle makarantu da harkokin kasuwanci, tare da hana tashin dubban jiragen sama, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito.
Guguwa ta kwashe rumfunahn tsugunnar da marasa galihu, wadanda ba su gidajen kwana, ta kuma kawo tsaiko wajen samar da man fetur, al’amarin da masanan yanayi suka yi wa lakabi da “Polar borted,” su kuwa kafafen yada labarai suka kakaba w ayanayin sunan “polar pig.”
Ma’aunin yanayin sanyin ya kama daga  Selshiyos 11 zuwa 22 a bangaren Montana da Rewaci da Kudancin Dakota da Minnesota da Iowa da Wisconsin da Michin da Nebraska, akmar yadda Cibiyar Kula da Yanayi ta kasa ta bayyana.
Fiye da rabin yawan jiragen da ke safara a babban filin jirgin saman Chigaco an dakatar da su, domin man da za a zuba musu ya daskare, don haka matukan jiragen ba za su iya cikan tankunansu ba. Maunin yanayin da yamma yakan kai digir selshiyos 24, inda ake samun tsananin sanyi a bangaren Antatika, don ma’aunin kan kai digiri 0 na selshiyos, a lokacin bazarar a Kudancin duniya (Sothern Hemisphere).