✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila na ci gaba da ruwan bama-bamai a Zirin Gaza

Jiragen saman yaki na Isra’ila sun ci gaba da yin ruwan bama-bamai a yankin Zirin Gaza da Yahudawa suka yi wa kawanya. Isra’ila ta nufi…

Jiragen saman yaki na Isra’ila sun ci gaba da yin ruwan bama-bamai a yankin Zirin Gaza da Yahudawa suka yi wa kawanya.

Isra’ila ta nufi matsugunai daban-daban na mayakan Saraya Al-Kudus, reshen soji na kungiyar Jihadul Islam da ke Zirin Gaza.

Kungiyar Saraya Al-Kudus ta ce ta fara kai hare-hare da makaman roka domin mayar da martani ga Isra’ila.

Kakakin Kungiyar Abu Hamza ya fitar da sanarwa ta shafinsa na Twitter cewa “Mun sanar da dakatar da kai harin martani kan Isra’ila saboda hare-haren da ta kai Gaza da Sham, amma makiyanmu sun ki cika alkawari inda suka kai wa matsugunanmu hari. Mu ma za mu ci gaba da mayar da martani.”

Rikici tsakanin Isra’ila da Gaza ya tsananta bayan da sojojin Isra’ila suka kashe wani mamban kungiyar Jihadul Islam a safiyar Litinin da ta gabata.

An harba makaman roka sama da 49 zuwa cikin Isra’ila daga Gaza, wanda hakan ya sanya Isra’ila yin ruwan bama-bamai kan sansanonin Jihadul Islam da ke Gaza da Sham Babban Birnin Siriya.

Sakamakon hare-haren an kashe mayakan Jihadul Islam biyu a Siriya inda aka jikkata wadansu hudu a Zirin Gaza.

A gefe guda kuma Firayi Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi alkawarin gina sababbin gidaje 3,500 ga Yahudawa ’yan kama-wuri-zauna a wani bangare mai matukar hadari da ke gabar Yammacin Kogin Jordan.

Ya ce tuni ya bada umarnin fitar da tsarin da ya kamata a yi amfani da shi wajen gina gidajen a wani wurin da ake kira E-1 da ke kusa da Birnin Kudus.

A baya dai an yi ta nuna adawa da irin wannan shiri da Isra’ila ke aiwatarwa.

Masu adawa da shirin na ganin cewa zai raba yankin na gabar Yammacin Kogin Jordan zuwa biyu.

Sai masu sharhi na ganin matakin Mista Netanyahu wata dama ce da za ta kara masa farin jini a wajen jama’ar kasar yayin da yake tunkarar zabe a mako mai zuwa.