Da Dumi Dumi

Iyalai da masoya sun kewaye asibitin da Mandela ke kwance

Tsohon Shugaban Afirka ta Kudu, Mista Nelson Mandela,  yana kwance a asibiti, inda iyalansa suka kewaye shi. Kuma dimbin al’ummar kasar sai wake-wake suke yi da nuna alhinin rashin lafiyarsa a gaban asibitin.
Kafofin yada labarai sun bayyana cewa, wasu masu kudi sun saki tantabaru 100 a gaban asibitin da Mandela ke kwance. Mutanen kasar da sauran al’ummar Afirka sun yi matukar nuna damuwarsu kan halin da Mandela tsohon dan kishin kasa, wanda ya yi fafutikar yaki da wariyar launin fata ke ciki.
Masu bayar da shawara a fadar White House, sun bukaci iyalan Mandela da ’yan uwansa da su shirya wa ziyarar da Shugaba Obama zai kai masa a asibiti.

Share