✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyalan Shugaba Mursi za su kai karar sojojin Masar

Iyalan Shugaba Muhammad Mursi, wanda aka hambarar da gwamnatinsa, sun zargi sojojin kasar da yin garkuwa da shi. ’Yarsa, Shaima ta kira wani taron ’yan…

Iyalan Shugaba Muhammad Mursi, wanda aka hambarar da gwamnatinsa, sun zargi sojojin kasar da yin garkuwa da shi. ’Yarsa, Shaima ta kira wani taron ’yan jarida a birnin Alkahira, inda ta bayyana cewa iyalan Mursi za su kai karar sojojin kasar.
An sakaya Mursi a wani boyayyen wuri da ba a bayyana ba, ba tare da an tuhume shi da wani laifi ba, tun bayan da aka hambarar da gwamnatinsa a ranar uku ga wannan wata na Yuli. Don haka iyalan hambararren shugaban kasar, sun bayyana cewa “tsaro da kariyar lafiyarsa” alhakinsu duk ya rataya a kan sojojin kasar. Wannan ita ce sanarwar farko da aka samu daga iyalan tsohon shugaban kasar.