✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyan Zazzau ya kai El-Rufai kotu kan nadin Sarki

Yana neman kotu ta soke nadin da El-Rufai ya yi wa Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau

Iyan Zazzau Alhaji Bashari Aminu, ya maka Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a kotu yana kalubalantar nadin Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau.

A karar da ya shigar gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna ta hannun lauyansa, Yunsu Usman, dan gidan sarautan na bukatar kotun ta soke nadin da El-Rufai ya yi wa Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, baya ga wasu bukatu guda tara da ya gabatar.

A ranar Laraba, 7 ga Oktoba — kasa da mako guda — Gwamna El-Rufai ya nada Ahmed Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19 wanda masu zaben sarki da gidajen sarautar Zazzau suka yi wa mubaya.

Jaridar Premium Times ta ce wani makusancin Iyan Zazzau ya tabbatar mata cewa El-Rufai da wasu mutum tare ne basaraken ke kara a gaban kotun.

Alhaji Bashari Aminu shi ne dan takarar da ya fi samun kuri’u cikin mutum uku da Masu Zabar Sarkin Masarautar Zazzau suka fara gabatar wa gwamnan ya zabi sabon Sarkin Zazzau a cikinsu.

Sai dai daga bisani Gwamnatin Jihar ta sanar da nadin Alhaji Ahmed Bamalli, tsohon Jakadan Najeriya a kasar Thailand, a matsayin sabon Sarki Zazzau.

Bamalli shi ne wanda Gwamnan Jihar ya amince da nadinsa daga cikin mutum 13 da suka nemi kujerar a zagaye na biyu da gwamnatin jihar ta umarci masu zaben sarki su yi.

Kafin nadin nasa, Gwamna Nasir El-Rufai ya bukaci a ba wa karin masu neman takara dama sannan a sake zaben, inda ya yi zargin saba ka’ida wajen tantance daya daga cikin ‘yan takarar.

Tirka-tirkar nadin Sarkin Zazzau na 19 ta taso ne bayan rasuwar Sarki Shehu Idris a ranar 20 ga Satumba, bayan ya shekara 45 a kan kujerar.