✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyaye sun koka kan gararambar da ’ya’yansu ke yi bayan rufe gidajen kangararru

Wadansu daga cikin iyayen yaran da aka ce an kubutar daga Makarantar Islamiyya ta Ahmad Bin Hambal da ke Layin Mai Dubun Tsumma a Rigasa…

Wadansu daga cikin iyayen yaran da aka ce an kubutar daga Makarantar Islamiyya ta Ahmad Bin Hambal da ke Layin Mai Dubun Tsumma a Rigasa da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna suna ci gaba da kokawa a kan gararanbar da suka ce ’ya’yansu ke yi bayan rufe makarantar da gwamnati ya yi.

A cewar iyayen, rufe makarantar da aka yi, yanzu wadansu yaran sun daina kwana gida ballantana su koma wata makarantar.

Suka ce dama can yaran ba su da tarbiyya mai kyau wanda hakan ya sa aka kai su makarantar domin gyara musu tarbiyya amma gwamnati ta je ta rufe makarantar.

Idan ba a manta ba, Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe irin wadannan gidajen horo, inda hakan ya sa ’yan sanda suka kai samame a cibiyoyin a jihohin Katsina da Kaduna da Kwara da Oyo da sauransu.

Sai dai bayan rufe gidajen da gwamnati ta yi, ba ta gina ko ta dauki alhakin kula da yaran ba, inda wadansu iyaye ke ganin ba a yi musu adalci ba.

Aminiya ta ziyarci Makarantar Ahmad Bin Hambal inda ta tattaunawa da wadansu daga cikin iyayen yaran da aka saki.

Malama Zainab Aliyu wadda aka fi sani da Maman Daddy ta ce danta Ahmad wanda yana daya daga cikin daliban makarantar ba ta gan shi ba kusan wata daya ke nan.

“Har yanzu ban gan shi ba domin bai dawo gida ba tun daga lokacin da ’yan sanda suka je aka kwashe su. Kuma dama abin da muke gudu ke nan. Domin akwai iyayen da har yanzu ba su ga nasu ’ya’yan ba.

“Akwai dan kanwata da ta rasu mai suna Abba wanda muka dauko shi daga Jos domin ganin maraya ne, sai muka kai shi makarantar kuma Malam Isma’il Shugaban Makarantar ya karbe shi ba tare da mun biya kudi ba, saboda a taimaka a gyara masa tarbiyya. Amma tun bayan rufe makarantar yanzu sun fara komawa gidan jiya, ma’ana sun fara shaye-shaye. Shi ma ba mu san inda yake ba a yanzu,” inji ta.

Ta bayyana damuwar cewa muddin ba a dauki matakin da ya dace ba, yaran na iya zama masu aikata manyan laifuffuka a cikin al’umma wanda gudun haka ne ya sa suka kai su gidan horon yara.

Ita ma Malama Bilkisu Ahmad cewa ta yi ’ya’yanta biyu suna nan gida babu abin da suke yi sai gantali a cikin unguwa.

“Ba mu jin dadin ganin yaran nan a gida ba su yin komai saboda mu ne iyayensu mun kuma san dalilin kai su irin wannan makaranta.

“Gaskiya da Gwamna ya san irin son da aka masa a baya, da bai yarda an rufe wajen nan ba. Domin a yanzu ji muke an cutar da mu, su kuma ’ya’yansu na can na karatu suna jin dadi, mu kuma ga namu nan sai yawo suke yi,” inji ta.

Da aka tambaye ta ko a shirye take ta sake tura danta makarantar idan aka sake budewa sai ta ce, “Ai mu jira muke yi kawai a sake budewa mu maida su domin a can fa addini da Sallah da Azumi ake koya musu. Ai so muke su gyaru.”

Shi ma Muhammad Abdullahi wanda ke da yaro Adamu a makarantar kusan shekara uku kafin a rufe ta cewa ya yi, “Ni da kaina na zo na rok, da kyar aka dauke shi amma bayan kai shi makarantar gaskiya na samu kwanciyar hankali, amma tunda aka rufe makarantar ba ni da kwanciyar hankali wanda hakan ya sa nake ganin wannan gwamnati ta zalunce mu.

“Wannan abu da makarantar ke yi ita gwamnatin ce ya kamata a ce ta yi mana. Sun kasa yi, mun zo mun roka wadansu na yi mana don ’ya’yanmu su gyaru amma gwamnati ta zo ta wargaza su.

“An fi so dai a ji ana cewa Musulmi su ne barayi, su ne ’yan Boko Haram ko masu garkuwa da mutane, in ba haka ba ai ba za a kawo wannan abu har su rusa makarantar ba,” inji shi.

Yusuf Isa daya ne daga cikin daliban makarantar da aka rufe ya kuma bayyana takaicinsa dangane da rufe makarantar da aka yi.

“Gaskiya ban ji dadi ba domin rufe makarantar ya lalata min tsarin karatuna saboda a yanzu ba batun neman kudi ba ne a gabana, neman ilimin addini ne. Amma sai ga shi sun je sun rufe mana makaranta duk sun watsa mu.

“A ina suke lokacin da muke shan kwaya muke sare-sare a cikin al’umma, sai a yanzu da iyayenmu suka kai mu makarantar domin a gyara mana rayuwa za su zo su rufe makarantar. Tun lokacin da muka fara karatu duk mun kama hanyar shiryuwa amma a yanzu wasunmu na neman komawa gidan jiya.

“Kwanan nan na samu labarin wadansu daga cikin daliban da aka kwashe daga makarantar sun yi wa wadansu mata fyade tare da kwace musu waya a wajen Gadar Kasuwar Barci kusa da Bankin UBA a Tudun Wada. Kuma ka san dai iyayenmu ne suka kai mu wannan cibiya ko makaranta domin a gyara mana tarbiyya wannan ya sa muke jira a bude makaranta mu koma,” inji shi.

Ya shawarci gwamnati ta sako musu malaminsu da ke tsare tun bayar rufe makarantar da aka yi, domin a cewarsa ba a yi masa adalci ba domin babu laifin da ya yi.

Shi ma wani dalibin makarantar, Abubakar Isma’il wanda ya ce, “An kai ni makarantar ce saboda ba na son yin karatu kuma ba na son zuwa makaranta shi ne iyayena suka kai ni. Kuma tun bayan rufe makarantar babu wani abu da nake yi sai yawo a unguwa,” inji shi.