✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyayen matasan da ‘yan sanda suka kashe a Kano na neman hakkin ‘ya’yansu

Kura ta lafa a unguwar Yar-Kuka dake yankin Sharada a cikin Kano bayan  jami’an ‘yan sanda dake karkashin sun hallak matasa.

Kura ta lafa a unguwar Yar-Kuka dake yankin Sharada a cikin Kano bayan  jami’an ‘yan sanda dake karkashin rundunar Anti-Daba sun hallaka matasa biyu a karshen  mako.

An dai zargi su ne da kashe matasan biyu, Abubakar Isah da Ibrahim Sulaiman ta hanyar harbe daya daga cikinsu yayin da dayan kuma suka daba masa wuka a gadon baya, har sai da ya ce ga garinku nan.

Lamarin dai ya tayar da kura da jawo zanga-zangar nuna Allah-wadai kan abinda aka zargi ‘yan sandan da aikatawa.

Sai dai iyayen yaran da iftila’in ya fadawa sun bukaci a yi musu adalci, ko da dai sun ce suna cike da rashin tabbas a kan hakan.

Malam Suleiman Ibrahim, wanda shine mahaifin marigayi Ibrahim Suleiman ya ce yin adalci kawai ta hanyar hukunta wadanda ke da hannu ne kawai zai sa hankulansu su kwanta.

Ya kara da cewa ‘yan sandan sun yi wa unguwar kawanya ranar Asabar da misalin karfe 9:00 na dare kamar yadda suka saba sannan suka kama Ibrahim da Abokinsa Abubakar sannan suka kashe su tun ma kafin a kai su ofis.

“Ba wanda ya fada dalilin da yasa aka kama su kafin a kashe su, har yanzu abin daure mana kai yake yi. Mun bibiyi a bamu bayani daga hukumomin ‘yan sanda amma har yanzu ba a ce mana uffan ba,” inji Malam Suleiman.

Ya ce bayan faruwar lamarin aka garzaya da su asibiti inda nan take aka tabbatar Abubakar ya mutu, yayin da shi kuma Ibrahim ya rasu a sibitin daga bisani.

Malam Suleiman ya ce lamarin na faruwa suka sanar da ofishin ‘yan sanda na unguwar Sharada wadanda suka kasance tare da su har aka binne mamatan.

Shima a nasa bangaren, Malam Musa Abdullahi wanda shine mahaifin Abubakar Musa cewa ya yi, “Ina so hukumomi su gudanar da bincike domin su gano laifin da wadannan yaran suka aikata da har suka cancanci hukuncin kisa. Ya kamata a yi adalci domin kaucewa faruwar hakan a nan gaba. Ba ma son wannan rashin adalcin ya ci gaba.”

An kama ‘yan sandan da suka yi kisan

Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar ya umarci a kame tare da tsare dukkan jami’an dake cikin tawagar kuma yanzu haka sun sashen binciken manyan laifuka inda ake zurafafa bincike a kansu.

Daga nan sai ya sahawarci jama’a kan su kwantar da hankulansu inda ya ce rundunar ta kudiri aniyar hukunta duk wanda suka tabbatar da hannunsa a ciki.

Idan za a iya tunawa ko a watan da ya gabata sai da makamancin wannan ya faru a unguwar Kofar Mata ta Kanon inda ‘yan sandan suka hallaka wani matashi mai suna Saifullahi yayin zanga-zangar #EndSARS.