Aminiya

Iyayen yara a Kano sun bukaci a sako yara 47 da aka sace

Iyayen yaran da aka sace ‘ya’yansu a Kano sun bukaci gwamnatin tarayya da ta jihar su tabbatar da an kubutar da karin wasu yara 47 da aka sace har yanzu ba a gansu ba, wanda ake zargin har yanzu suna Kudu bayan sace su daga Kano.

Wasu dai kungiyoyi sun bayyana cewa, an wasu bata gari da suka shahara wajen satar yara musulmi daga Kano zuwa Kudu a sayar dasu sannan a bautar da su tare da sauya masu addini.

ADVERTISEMENT

Iyayen yaran sun yi kiran ne a karkashin kungiyar da ke kwato ‘yancin yaran da aka sace da kuma wadanda suka bace don binciken gano inda suke.

Sakataren kungiyar Malam Shuaibu Ibahim, ne ya sanar da hakan ya ce iyayen yaran da aka sace suna cikin wani mummunan yanayi saboda rashin ‘ya’yan su.

ADVERTISEMENT