✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Izala ta zargi Iran da goyon bayan ta’addanci

kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa ta nuna goyan bayanta, kan yadda wasu kasashen suka yanke huldar jakadanci da kasar Iran kan…

kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa ta nuna goyan bayanta, kan yadda wasu kasashen suka yanke huldar jakadanci da kasar Iran kan takkadamarta da kasar Saudiyya.
Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da wa’azi, a Masallacin Juma’a na ’Yan taya da ke garin Jos, inda ya ce: “Muna goyan bayan kasashen da suka yanke hulda da kasar Iran, domin kasar Iran ba ta da adalci kuma tana goyon bayan aikata ta’addanci a duniya. Misali irin abin da ya faru a kasar Saudiyya na zartar da hukuncin kisa ga malamin Shi’ar nan Sheikh Nimr al-Nimr da wasu mutum 46 da aka samu da laifin ta’adanci a Saudiya, amma sai Iran ta fito tana ta ihu kan wannan al’amari duk da ta san Saudiya kasa ce mai ’yancin kanta.”
Sheikh Jingir ya ce a nan Najeriya a kwanakin baya, ’yan Shi’a sun tare hanya suka hana shugaban sojin Najeriya Janar Tukur Burtai wucewa, inda yin haka ya kawo rikici tsakaninsu da sojoji, amma sai Iran ta fito tana sukar Najeriya, duk da ta san cewa Najeriya kasa ce mai ’yancin kanta.
Ya ce wadannan abubuwa da Iran take yi wa kasashen Musulmi akwai raini a ciki kuma ya nuna tana gaba da addinin Musulunci ne.
Daga nan sai Sheikh Jingir ya yi kira ga gwamnonin jihohin Arewa kan su dubi batun mutanen da ke tsare a gidajen yari a jihohinsu ba tare da wani laifi ba, don ganin sun taimaka an sako su.
Ya yaba wa gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan nasarorin da ta fara samu a kasar nan, musamman dawo da zaman lafiya da kuma inganta samar da man fetur.