Search
Subscribe
Jacob Zuma ya daukaka kara

Jacob Zuma

Jacob Zuma ya daukaka kara

Shari’ar da aka jima ana dakon zuwanta ta tsohon ShugabanAfirka ta Kudu, Jacob Zuma, an dage ta zuwa badi bayan da lauyoyinsa suka ce za su daukaka kara kan hukuncin da kotu ta yanke na ci gaba da sauraren tuhume-tuhumen da ake yi masa da suka jibanci yarjejeniyar makamai.

“Mista Zuma yana da nufin yin amfani da ’yancin da tsarin mulki ya ba shi na damar daukaka kara,” inji Lauyansa Thabani Masuku, wanda ya bayyana haka ga alkalin da ke sauraren tuhumar Mista Zuma a wata Babbar Kotun yankin Pietermaritzburg.

Ko a ranar Juma’ar da ta gabata, kotun ta yi fatali da bukatar da Zuma ya gabatar ta a dakatar da sauraren shari’ar tasa kwata-kwata, inda ya shigar farkon bana.

Zuma na da kwana 15 don ya mika hanzarinsa na cewa kada a ci gaba da sauraron shari’ar. Kuma sai ranar 22 ga Nuwamba ne za a saurari hanzarin nasa.

Lauya  Billy Downer da yake magana a madadin lauyoyin gwamnati ya bayyana cewa: “Lallai ne gwamnatin kasar ta kalubalanci bukatar ta Mista Zuma.”

Ya ce a watan Afrilun badi ne za a bayyana sabuwar ranar gurfanar da Mista Zuma, kuma cikin kwana 16 ya kamata ya mayar da martani  ga zarge-zargen cin hanci da yin wadaka da dukiyar kasa da badakalar nan da ta jibinci sayen makamai daga wasu kamfanonin Turai a karshen shekarun 1990, da aka sani da lakabin ‘Yarjejeniyar Makamai.’ Sai da tsohon Shugaban, ya musunta aikata ba daidai ba.

Bayan sauraron tuhumar, Mista Zuma wanda yake cikin annashuwa ya yi wa taron daruruwan magoya bayansa da suka hallara a gaban kotun, jawabi, inda ya ce: “Za mu dawo nan, za mu dawo, kuma za mu dawo nan,” lokacin da yake jawabi ga cincirindon magoya bayansa da suke raye-raye, bisa alama yana nuna cewa zai koma kotun ce domin ya daukaka kara.

Dadadden al’amari ne

Ko hanzarin da Zuma zai gabatar zai taimaka wa Afirka ta Kudu wajen yaki da cin hanci?

A shekarar 2005 ne dai aka fara nuna yatsa ga Zuma dangane da zarge-zargen cin hanci da suke da nasaba da sayen makamai daga kamfanonin kera makaman a Nahiyar Turai, ciki har da na Thales.

Zarge-zargen da ake masa sun hada da yin coge wajen biya ko karbar kudade sau 783 da ake zargin ya aikata a tsakanin 1996 da 2005 ta hannun Mataimakinsa ta fuskar kudi a lokacin, Shabir Shaik, wanda aka yanke wa hukuncin daurin shekara 15 a gidan yari a 2005.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin