✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jagoran Fulani Alhaji Sale Bayari ya zama Bauran Wase

Mai martaba Sarkin Wase da ke Jihar Filato, Alhaji Muhammad Haruna Sambo, ya nada Shugaban Kungiyar Ci Gaban Al’ummar Fulani ta Najeriya ta Gan Allah…

Mai martaba Sarkin Wase da ke Jihar Filato, Alhaji Muhammad Haruna Sambo, ya nada Shugaban Kungiyar Ci Gaban Al’ummar Fulani ta Najeriya ta Gan Allah Alhaji Sale Bayari a  sarautar Bauran Wase . An yi bikin nadi ne a fadar Sarkin  da ke garin Wase a ranar Asabar  da ta gabata.

Da yake jawabi a wajen bikin Sarki Muhammad Haruna Sambo, ya ce babban abin da ya sa masarautar ta karrama Alhaji Sale Bayari da sarautar Bauran Wase, shi ne saboda irin ayyukan da ya yi a masarautar shekaru da dama da suka wuce na kare hakkokin al’ummar Fulani da kuma magance matsalolin da suke faruwa a tsakanin Fulani makiyaya da manoma a Najeriya.

“Wannan karramawa da muka yi wa Alhaji Sale Bayari na nada shi Bauran Wase, mun biya shi bashi ne na abubuwan alherin da ya yi wa wannan masarauta. Don haka muna kira ga al’ummar wannan masarauta, su yi koyi da wannan bawan Allah, domin duk da cewa shi ba dan wannan masarauta ba ce, amma ya nuna mana shi dan wannan masarauta ce, ta abubuwan da ya yi na ayyukan alheri,” inji Sarkin

Sarkin ya ce yanzu ana yaki ne da ilimi, don haka ya yi kira ga al’ummar masarautar su tashi su nemi ilimi, domin a samu ci gaba a masarautar da kasa baki daya.

Da yake jawabi bayan kammala nadin, Bauran Wase Alhaji Sale Bayari ya ce  bai san irin kalmomin da zai iya bayyana farin cikin da ya yi ba, kan wannan nadi da aka yi masa.

Ya ce wannan babbar sarauta da aka ba shi ba karamin abu ba ne, don haka ya yi matukar farin ciki.

Ya ce, wannan sarauta za ta karfafa masa gwiwa kan abubuwan da yake yi  wadanda mutanen Wase suka gani suka ba shi wannan sarauta.

Shi dai wannan bikin nadi ya samu halartar Mai martaba Sarkin Dukku Alhaji Haruna Rashid II da sauran manyan Sarakuna da shugabannin al’ummar Fulani daga kowanne bangare na Najeriya.

Kuma a wannan rana da aka gudanar da wannan nadi an yi bikin ranar Fulani a garin Wase, inda aka gudanar raye-raye da kade-kade da wake-wake na al’ummar Fulani.