✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jagoranci a harkar kasuwanci (7)

  Shawara ta Bakwai: dan kasuwa a matsayinsa na shugaba zai kasance mai daukar kasada daidai gwargwadon iko; kuma idan ya dauki kasada domin cim…

 

Shawara ta Bakwai:

dan kasuwa a matsayinsa na shugaba zai kasance mai daukar kasada daidai gwargwadon iko; kuma idan ya dauki kasada domin cim ma wani buri, al’amarin da ya yi niyya bai kai ga nasara ba, to ya kasance mai yarda da kuskurensa ga mabiyansa. daukar kasada ya zama dole a dukkanin al’amura na rayuwa da ake bukatar a samu cigaba a cikinsu. Da gwaji jirgin sama ya tashi, inji  Bahaushe. Kasada a nan na nufin yin  wani abu sabo wanda ba ya cikin al’adar abin da aka saba yi yau da kullum, kuma wanda ba a da tabbacin sakamakonsa.
Kasada na iya kasancewa a fannoni daban-daban. Tana iya zuwa a rungumar wata sabuwar hajja da ba a santa a kasuwa ba. Misali, sai ya kasance dan kasuwa na harkar sayar da kayayyakin inganta dandanon miya, wato abubuwa irin su magi da makamantansu. Sai ya kasance irin wadannan abubuwa a kasuwa sun hada da Magi mai tauraro  da mai zakara da Knorr da wadansu makamantansu. Sai kwatsam wani kamfani ya zo da sabon irin wannan abin miya  mai suna ‘Zakwai Mai Zabo’. Mu yi tsammani dan kasuwarmu a kasuwar Abubakar Rimi yake a Kano, kuma wannan kamfani na bukatar babban dillali a wannan kasuwa da zai kasance mai sayar wa da sauran ’yan kasuwa wannan hajja tasa, saboda haka ya  zo ga dan kasuwarmu ganin karfin da yake da shi a wannan harka. Wannan kamfani ya kuma tsayar da ka’idar cewa babban dillali sai ya ajiye Naira miliyan daya a wurinsa, ya kuma sayi katan dubu daya na wannan hajja tasa.
Wata kasadar kuma na iya kasancewa a fannin bayar da lamuni. Wani babban abokin ciniki na iya zuwa ya nemi dan kasuwa ya lamunce shi wadansu daga cikin kudin kayan da ya saya; watau ya biya wadansu kudaden a wannan lokacin, ya kuma biya sauran a gaba. Wata kuma kafar da kasada ke iya zuwa ga dan kasuwa a matsayinsa na shugaba ya yanke hukuncin fuskantar ta, ita ce ta fadada harkarsa, walau ta sake bude wadansu wuraren tafiyar da harkarsa, ko kuma ta wani sabon tsarin tafiyar da ita sabanin yadda yake yinta da.
Akwai hanyoyin da kasada ke iya samun dan kasuwa da yawa, fiye da wadanda na ambata. Yanzu bari mu duba yadda dan kasuwa zai fuskanci wadanda na jera. Shawara ga dan kasuwa jagora ita ce, yana da kyau ya tuntubi mabiyansa a duk lokacin da kasada irin wannan ta fado masa. Zai fada musu, ya fahimtar da su fahimtarsa da yadda al’amarin yake; wato fa’ida da rashinta na daukar wannan kasada, domin ya samu ra’ayin kowa daga cikinsu. Misali, batun Zakwai Mai Zabo, dan kasuwa zai nuna musu irin ribar da za a iya ci ta dogon lokaci idan ya karbi dillancin wannnan abin miya, kuma hajjar ta karbu a kasuwa. Zai kuma nuna musu wahalhalun yadda yake ganin za su iya samu wajen shigar da ita kasuwa har ta karbu kafin a fara cin gajiyarta.
dan kasuwa zai kuma duba yuwuwar rashin karbuwar wannan hajjar a kasuwa da irin asarar da za a iya yi idan ba ta karbun ba. A nan kuma zai saurari dukkanin ra’ayoyi da shawarwarin ma’aikatansa, sannan ya yi amfani da basirarsa ya yanke hukunci. A nan ina tsammani zai yi amfani da duk basirunsa na kasuwanci a kan hajjar kafin ya karba ko ya ki karba, wadanda suka hada da kabar sanfurin hajjar ya nuna wa sauran ’yan kasuwa masu irin wannan harka da yake tsammanin sayarwa idan ya karba, domin samun ra’ayinsu. Yana ma iya ba mata masu girki su yi amfani da ita domin sanin karbuwarta da ingancinta idan an gwada da sauran irinta da ke kasuwa.
Sarari a wannan filin ba zai bar ni in kara misalai a kan kasadun da na jera ba, amma idan dan kasuwa ya kamanta su da misalin da na bayar zai gamsu ya kuma amfana da yin hakan.

Babu wanda ya kwashe kayansa daga kasuwar Allah-gatan-kowa      – Idris Darakta

Abubakar Haruna, Daga Legas

Shugaban kasuwar gwanjo ta Allah-Gatan-Kowa da ke jihar Legas, Alhaji Idris Darakta ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa ’yan kasuwar sun fara kwashe kayansu suna barin kasuwar sakamakon ikirarin da gwamnan jihar ya yi na rushe kasuwar nan gaba.
A kwanakin baya ne dai gwamnan jihar Legas, Babatunde Raji Fashola ya kai ziyarar ba-zata kasuwar inda a jawabin da ya yi wa ’yan kasuwar ya yi ikirarin rushe kasuwar.
Alhaji Idris Darakta wanda har ila yau shi ne sarkin kasuwar, ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon da ya gabata, inda ya ce wadansu mutane ne ke yada jita-jitar don nuna kiyayyar su ga alherin da ke gudana a kasuwar.
Ya ce, ‘A gaskiya ni da nake magana da kai kamata ya yi ka ji magana daga bakina abin da wadansu mutane suke yi mana ba ma jin dadinsa. Mutum ne ba sana’a yake yi a cikin kasuwar nan ba amma sai ya rika yada maganar da ba haka take ba. Masu yada irin wannan jita-jita aniyarsu ta bi su domin ba masoyan kasuwar nan ba ne. Mu dai kasuwa idan gwamnati ta tashi rushe ta to mu za ta kira, domin gwamna da kansa ya ce idan ya tashin yin aiki zai tuntube mu mu, ma kuma idan muna bukatar wani abu mu tuntubi wakilansa. Mun je mun samu wakilansa, mun rubuta musu takarda kuma suka mayar mana da martanin cewa duk lokacin da suka tashi za su neme mu. To har yanzu ba su neme mu ba. Saboda haka wannan jita-jita ce kawai kuma maganar banza ce. Babu wani dan kasuwa da ya kwashe kayansa.’
Ya ci gaba da cewa, tun lokacin da gwamna Fashola ya ziyarci kasuwar kuma ya yi ikirarin rushe ta ya yi alkawarin tafiya tare da ’yan kasuwar kafada da kafada.
Ya bayyana cewa gwamnan ya yi mamaki a lokacin da aka shaida masa cewa kasuwar  ta yi kimanin shekar 36 tana ci kuma ta hada nahiyar Afirka tare da samar da kudin shiga ga gwamnatin jihar.
Ya kara da cewa, tun lokacin da gwamna Fashola ya yi ikirarin tayar da kasuwar suka mayar da al’amarinsu ga Allah da Ya zabar musu mafi alheri.
‘Tun lokacin muke ta yin addu’a, idan tashinmu za a yi to Allah Ya sa haka shi ne mafi alheri a gare mu, idan kuwa ba tashinmu za a yi ba to Allah Ya sa haka shi ya fi.’ Inji shugaban.