✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jagoranci a harkar kasuwanci (8)

Shawara ta takwas, kuma ta karshe: dan kasuwa ya kasance mai nuna annashuwa a matsayinsa na shugaba a duk lokacin da aka cimma wata nasara.…

Shawara ta takwas, kuma ta karshe: dan kasuwa ya kasance mai nuna annashuwa a matsayinsa na shugaba a duk lokacin da aka cimma wata nasara. Wannan zai ba ma’aikatansa ko wadanda yak e jagoranta karfin gwiwar cigaba da azama a gudunmawar da suke bayarwa wajen bunkasa al’amarin da aka sa gaba.
Annashuwa na iya kasancewa a siga da dama: Tana iya kasancewa fara’a ko murmushi ko ma dariya, ta yadda za a nuna farin ciki ga abokan tafiyar da harka, a kuma bayyana musu dalilin yi hakan. Misali, sai dan kasuwa ya yi lissafi ya ga an samu wata kyakkyawar riba a kan wata hajjar da aka sayar, to a nan yana iya fuskantar ma’aikatansa da kyakkyawar fuska ta murmushi ko dariya ya sanar da su cewa ga abin da ya faru, domin farin cikinsu gaba daya. A wannan yanayi ana iya yin addu’a a gode wa Allah a kan nasarar da aka samu. dan kasuwa na iya raba wa ma’aikatansa wadansu ‘yan kudi daidai gwargwadon iko daga ribar da aka samu, ko kuma ya sayi wadansu abubuwa ya raba musu kyauta domin su ma su ji dadi. Wannan zai sa su yi murna su kuma ji dadin cewa shugabansu yana la’akari da gudunmawar da suke bayarwa.
Haka kuma, dan kasuwa na iya yin irin wannan kokarin yayin da ya samu wata nasarar da ba ta samun riba kai tsaye ba, misali a ce an samu sayar da wata hajja da ta dade ba a sayar ba. Ko kuma an samu wani lasisin shigo da kaya daga kasashen waje da aka dade ana nema. Ko ma a ce an samu wata dama ta samun wata haja daga wani kamfani da za a iya samun alheri daga gare ta. To a nan ba sai dan kasuwa ya sayi wani abu ya ba ma’aikatansa ba, ko ya debi kudi ya ba su ba, amma ya zo gare su da murna ya shaida musu abin da ya faru ma wani abu ne da zai inganta goyon bayan da suke ba jagorancinsa.
A manyan harkoki kamar kamfanoni da bankuna, a kan ware wani kason ribar da harkar ta samu a shekara ko rabin shekara, misali a ce kashi goma daga cikin dari na ribar da aka samu, a raba wa ma’aikata a matsayin garabasa (bonas). Irin wadannan harkoki kuma na ba ma’aikatansu kyaututtuka a karshen shekara da kuma lokutan bukukuwa na addini da na al’ada, kamar Sallah da Kirsimeti da dai lokutan shagulgula irin haka. Irin wadannan kyaututtuka na kasancewa kudi ko sutura, ko kuma kayayyakin abinci. Akwai ma wata kyautar shekara ta al’ada da irin wadannan kamfanoni ke ba ma’aikatansu a karshen shekara da ake ce wa ‘Albashin watan 13’. To lallai babu watan 13 a lissafin shekarar Nasara ko ta Musulunci, illa dai kawai wata dabarar ‘yan kasuwa ce ta bai wa ma’aikatansu wani tallafi a karshen kowace shekara, wanda suke bayarwa a watan 12 na kowace shekara.
Kamfanoni irin wadannan kuma su kan kirawo taron walima a wadansu lokuta, musamman ma a karshen shekara, ko kuma a karshen shekarar kudin kamfanin. Ana wadata irin wannan walima da abinci iri-iri da kayayyakin sha na alfarma, wadansu lokutan ma da makada da mawaka, domin ma’aikata da shugabanninsu da masu kamfanin su ci su sha, su kuma nishadantu tare. Wannan cudanya na sa wa, ko kara fuskantar juna tsakanin ma’aikata da shugabanninsu da masu kamfanin, wannan kuma zai inganta gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa wajen habaka harkokin kamfanonin, domin za su ga kansu kamar masu kamfanin maimakon leburorin kamfanin da ba su da wani kaso a ciki.
dan kasuwa na iya kamanta irin wadannan kyautuka ga ma’aikatansa daidai karfinsa. Zai kuma iya hada walima ya kira ma’aikatansa a lokutan bukukuwa irin wadannan. Misali, zai iya kiran ma’aikatansa walimar  bude-baki a lokcin azumi.