Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Jahilci ya taimaka wajen rikice-rikicen da ake yi a Najeriya – Kwankwaso

Sanata Mohammed Kola Balogun da Alhaji Danjuma Yakubu

Jahilci ya taimaka wajen rikice-rikicen da ake yi a Najeriya – Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce jahilci ya taimaka wajen tashe-tashen hankula a kasar nan, inda ya ce, koyar da ilimin addini ga kananan yara zai taimaka wajen kawo karshen wannan matsala. Ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a wajen bikin kaddamar da asusun neman gudunmawar kudi domin gina wata Makarantar Islamiyya mai suna Al-Madaratul Nurul Islam Kwankwasiya a Unguwar Sabo, Ibadan. Ya ce “Saboda haka nake kira ga al’ummar Musulmin Najeriya su tashi tsaye wajen yawaita gina makarantun Islamiyya domin ’ya’yansu su koyi ilimin addininsu da na zamani wadanda su ne za su taimaka ga rayuwarsu a nan gaba.”

Ko’odinetan Kwankwasiya na Kasa, Alhaji Umar Mukhtar Yarima ne ya wakilci tsohon Gwamnan a wajen taroN, wanda makarantar ta yi amfani da shi wajen yaye dalibanta da suka haddace Izifi 5 zuwa 60 tare da daura auren ’yar Shugaban Makarantar Sheikh Ibrahim Nahantsi.

Injiniya Rabi’u Kwankwaso, ya nuna bakin ciki kan rashin halartar wannan taro, inda ya yi alkawarin ci gaba da bayar da tallafi ga makarantar domin daukaka kalmar Allah. Ya nemi attajirai da masu hannu da shuni su yi amfani da dukiyarsu wajen gina irin wadannan makarantu a sassan kasar nan a matsayin sadakatul-jariya, inda ya ce yin haka zai taimaka wajen taimakon ’ya’yan Musulmi sanin ilimin addininsu da kawo karshen matsalolin da kasa ke ciki ta fannin zamantakewar al’umma.

Shi kuwa Sanata Mohammed Kola Balogun da ke wakiltar Oyo ta Kudu, cewa ya yi hadin kai  a tsakanin kabilun kasar nan ne zai taimaka wajen kawo karshen rikice-rikicen da wadansu tsirarrun mutane suke haddasawa domin cimma burinsu.

Ya ce, akwai dadaddiyar zamantakewa a tsakanin jihohin Oyo da Kano ta fannonin kasuwanci da auratayya wadanda su ne kan gaba wajen yawan jama’a fiye da sauran jihohi. Ya yi fatar dorewar haka domin tabbatar da dunkulalliyar kasa. A jawabin maraba, Shugaban makarantar Sheikh Ibrahim Nahantsi ya yi wa bakin da suka halarci taron godiya inda ya jinjina wa Sanata Rabi’u Kwankwaso kan taimakon da yake bayarwa ga makarantar.

Ya yi kira ga jama’a Musulmi su yi koyi da shi a wannan fanni domin daukaka kalmar Allah. Sarakunan Hausawa da manyan malaman darikun Tijjaniya da Kadiriyya da na kungiyar  Izala da shugabannin kungiyoyi daban- daban da wadansu ’yan siyasa ne suka halarci  wannan biki.