✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jaje kan kisan sojojin Najeriya

Salam Edita da fatan kana lafiya, zan mika sakon jajantawata ga Rundunar Sojin Najeriya bisa mummunan harin da kungiyar Boko Haram ta kai musu a…

Salam Edita da fatan kana lafiya, zan mika sakon jajantawata ga Rundunar Sojin Najeriya bisa mummunan harin da kungiyar Boko Haram ta kai musu a garin Metele a Jihar Borno wanda ya yi sanadiyar rasuwar sojoji masu yawa. Babu shakka wannan babban abin takaici ne kuma kalubale ne ga Rundunar Sojin Najeriya da Gwamnatin Tarayya kan ikirarin cin galaba a kan kungiyar da suka dade suna yi. Muddin ana son shawo kan wannan kisan kiyashi da ake yi a sassa daban-daban na Najeriya to ya zama wajibi gwamnatin Najeriya ta sake sabon salon yaki da ’yan ta’addan ta hanyar samar musu da makamai na hakika da kuma biyansu hakkokinsu a kan kari, domin babu ranar da jami’an tsaron Najeriya za su ci galaba a ka ’yan ta’adda ba tare da samar musu da makamai na hakika da kuma biya su hakkokinsu ba!

Daga Ashiru Lawal Nagoma Ruwan Baure (Dan Kishin Talaka) Karamar Hukumar Gusau, Jihar Zamfara. 07086868025.