Da Dumi Dumi

Jama’a na tserewa daga yankin rainon Ingila na Kamaru

Mista Sisiku Julius Ayuk Tabe, Shugaban ’Yan tawayen yankin Ingilishi na Kamaru
Mista Sisiku Julius Ayuk Tabe, Shugaban ’Yan tawayen yankin Ingilishi na Kamaru

Dubban mazauna yankin rainon Ingila a Jamhuriyyar Kamaru sun tsere daga gidajensu kafin fara aiwatar da dokar hana zirga-zirga da ’yan tawayen Ambazoniya suka sanar.

An samu rudani a tashoshin motoci sakamakon cinkoson jama’a, lokacin da jama’a ke kokawar hawa motocin da za su bar garuruwansu saboda tsoron kada dokar ta fara aiki suna can.

A makon jiya ne mayakan  sa-kai na Ambazoniya suka bayyana lokacin zanga-zangar nuna rashin amincewa da hukuncin daurin rai-da-rai da wata kotun sojin kasar ta yanke wa jagororinsu 10 da suka hada da Sisiku Ayuk Tabe.

Sisiku Julius Ayuk Tabe dai shi ne ya jagoranci mutanen da suka ayyana kasar Ambazoniya, a matsayin kasa mai ’yanci kanta, inda ya bayyana kansa a matsayin  Shugaban Kasar na rikon kwarya na farko.

Yankin rainon Ingila na zargin Jamhuriyyar Kamaru da mayar da shi saniyar ware da kuma fifita masu magana da Faransanci a kan masu magana da Ingilishi.

ADVERTISEMENT

Rikicin yankin rainon Ingila dai ya fara ne a shekarar 2016, lokacin da lauyoyi da malaman makaranta suka tsunduma cikin wani yajin aiki na kin amincewa da kokarin da gwamnati take yi na saka musu harshen Faransanci a makarantu da kotuna a Arewa maso Yamma da Kudu maso Yammacin kasar Kamaru.

Wadansu mazauna yankin sun dauki makamai a shekarar 2017, inda daruruwan mutane suka mutu, fiye da mutum dubu 500 suka bar mahallansu.

Share