✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jamá’a na ture-reniyar fita daga Gama

Bayan kammala zaben gwamna da aka yi a Jihar Kano an sami mutane suna fitar farin dango daga mazabar Gama.. Mazabar Gama mazaba ce da…

Bayan kammala zaben gwamna da aka yi a Jihar Kano an sami mutane suna fitar farin dango daga mazabar Gama..
Mazabar Gama mazaba ce da ke da kuriu sama da dubu 49 wanda hakan ya janyo dukkanin ‘yan jamiyyun biyun APC da PDP suka mayar da hankali akanta.
Aminiya ta kai ziyarar gani da ido a wannan mazaba ta Gama daidai misalin karfe 3:40pm bayan an kammala zaben ana kidaya kuriu Aminiya ta ga yadda samarin yankin dauke da makamai da suka hada da gorori da gariyo suke ta murna cewa APC ta ci zabe a yanki.
Har ila yau Aminiya ta lura da yadda gungun mutane suke fita daga yankin wanda jamaar yankin suka ce dama can baki ne wadanda aka yi hayarsu daga wasu wurare don tayar da zaune tsaye a yankin.
Alhaji Yau Gama ya shaida wa Aminiya cewa “duukanin mutanen da ke fita daga yankin ba yan wurin ba ne su ne wadanda aka dauko don tayar da fitina a yanki. Yanzu haka sun gama abin da za su yi shi ne yanzu suke fita. Dama tun a wajen sallar Asuba muka kula da bakin fuskoki a yanki? ”
A cewar majiyarmu wadannan mutane da aka kawo mazabar ba zabe suka yi ba illa sun hana duk wani dan PDP yin zabe a yankin.
Wani abu da ya Aminiya ta lura da shi shi ne babu wani mutane da za ka gani masu dauke da wata alama da ke nuni a matsayin ejen na jamiyyar don gudun abin da zai biyo baya.