✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jama’ar Kenya na jimamin harin cibiyar kasuwanci ta Westgate

kwararrun masana kan harkar sarafa nakiya da gurneti da dasa bama-bamai, suna gudanar da bincike a cibiyar hada-hadar kasuwancin westgate ta kasar Kenya, inda aka…

 Wata daga cikin wadanda aka ceto a harin Kenyakwararrun masana kan harkar sarafa nakiya da gurneti da dasa bama-bamai, suna gudanar da bincike a cibiyar hada-hadar kasuwancin westgate ta kasar Kenya, inda aka shafe kwana hudu ana zubar da jini, tsakanin ‘’yan biniga da sojojin kasar. Har yanzu dimbin mutane sun kace, bayan da aka hallaka mutum fiye da 70, aka jikata wasu fiye da mutum 100.
“Suna gudanar da binciken don gudun ko maharani sun nasa nakiya, ko wata na’urar tada bama-bamai,” a cewar wata majiya daga jami’an tsaron kasar, kuma an sanya mutum-mutumin mai kwakwalwa na Robot yana kewaya wurin.
Wakilin Kamfnain Dillancin Labarai na AFP da ke sanye da rikar sulke a gefen kafatariyar cibiyar kasuwanci, ya ce ya hango gungun karnuka masu sansano nakiya, suna ta binciken inda aka nasa bama-bamai, tare da neman inda wasu mutum 60 suka shiga.
Shugaban kasa Uhuru Kenyatta, ya bayyana cewa, fatan da aka fafata, a garkuwar da aka yi da mutane na tsawon sa’o’i 80 ya kawo karshe, tare da dimbin asarar rayuwa, wadanda suka hada da jami’an tsaro shida.
Maharan da aka fatata da su sun kai a kalla 10 zuwa 15, kamar yadda wani Muhammad ya bayyana a shirin gidan talabijin na Amurka, mai taken “PBS Newshour,” kuma a cewarsa, shekarunsa duk ba su wuce 18 zuwa 19 ba. Mafi yawansu ’yan Somaliya ne ko Larabawa, sannan sun kasance mazaunan Amurka, a wani wuri da ke Minnesota da sauran wurare,” inji shi.
Sakataren Harkokin tsaron Birtaniya ya bayyana cewa akalla mutum shida ’yan Birtaniya suka mutu a harin da aka kai. Sauran kasashen da suka hada da Sin da ghan da Faransa sda Nezalan da Kanada, jami’an Gwamnantin Kenya sun bayyana cewa sun yi asarar akalla mutum 62. Ana ta yada jita-jita kan maharani, inda aka bayyana cewa har da Amurkawa. Don haka Gwamnatin Amurka t ace za ta ci gaba das a ido kn wadand ake horar da ’yan ta’adda.
daya daga cikin maharani da suka mamaye Cibiyar Kasuwanci ta Westgate, an bayyana cewa akwai wata Baturiya, a cewar majiyar jami’an asirin Kenya, a hirar da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters. Sai dai wasu na ganin majiyar ta bayyana hakan ne don ta jefa shakku ko bincike kan ko an halaka matar daka kashe wa miji a Birtaniya, wadda kafofin yada labaran Birtaniya ke yi wa lakabi da “White Widow,” wato Samantha Lewthwaite. Da ma jami’an tsaro na nemanta ruwa a jallo, bisa zargin shirin kai hare-hare a wuraren sayar da abinci da otal-otala a kasar Kenya. Da ka tambayi jami’in asirin ko wannan Baturiyar ita ce Misis Lewthwaite, sai ya ce: “Ba mu da masaniya.”
Masana dai sun bayyana cewa, tun daga Aljeriya zuwa Najeriya har Kenya, akwai gungun ’yan bindiga da ke hare-hare, inda suke fakewa da talaucin da al’umma ke fama da shi da rikice-rikice da rashin daidaito, ta inda suke ruruta wutar kiyayya ga Yammacin Turai da koyarwar addinin Kirista. Kuma wadannan matsaloli su ne hukumomi da hukumomin duniya ke kawo wa cikas wajen bunkasa tattalin arziki da harkokin siyasa.