✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jamhuriyyar Benin ta fara kidayar ’ya’yanta da ke Najeriya

Jamhuriyar Benin ta fara  kidayar ’y’ayanta da ke zaune a Najeriya. Bayan kammala aikin na mako uku a Najeriya za a ci gaba da yin…

Jamhuriyar Benin ta fara  kidayar ’y’ayanta da ke zaune a Najeriya. Bayan kammala aikin na mako uku a Najeriya za a ci gaba da yin irinsa a kasasashen Afirka kamar yadda Kungiyar Tattalin Arziki ta Afirka (ECOWAS) ta nemi a yi.

Da yake yin bayani a ranar Lahadin da ta gabata a Ibadan Mataimakin Sakatare Janar na Gwamnatin Benin, Mista Cyrille Gobgbedji ya ce “Mun zo ne bisa umarnin gwamnatinmu na tantance al’ummarmu da yi musu rajista da kidaya su a Najeriya don tabbatar da cewa kowa ya mallaki katin shaidar zama dan Benin domin kyautata zamantakewa da tsaron lafiyar al’ummomin  kasashe da ke makwabta da juna.”

Mista Cyrille Gobgbedji, wanda ya jagoranci manyan jami’an gwamnatin Benin da suka hada da mai bayar da shawara a ofishin Ministan Harkokin Waje Mista Benoit Adekambi da Jakada Adegnanju da daruruwan ma’aikatan da za su yi aikin kidayar sun yi wa dimbin ’yan kasar Benin mazauna Jihar Oyo bayani game da muhimmancin mallakar katin shaidar zama dan kasar Benin, inda suka tabbatar masu cewa gwamnatin kasarsu ba za ta yi komai wajen karbo duk dan kasar da aka kama a Najeriya ba tare da ya mallaki katin shaida ba.

“Dalilin zuwanmu Najeriya ke nan domin yi muku rajista da kidaya ku. Saboda haka muke kira ku tabbatar kun isar da wannan sako ga sauran jama’a da ba su samu halartar wannan taro ba,”inji Mista Gobgbedji.

Ya ce a cikin watan farko na badi za a fara aikin rajistar dukkan jarirai da ’yan kasar Benin suka haifa a sassan Najeriya. Ya yi kira gare su tabbatar da kare mutuncin kasarsu ta fannin girmama dokokin Najeriya.

Aminiya ta zanta da Sarkin al’ummar Benin a Jihar Oyo Alhaji Salisu Ibrahim, wanda ya nuna farin ciki da rajistar kidayar jama’arsu da mahukuntan kasarsu suka bullo da ita. Ya ce, “Hakan zai taimaka kwarai wajen dakile miyagun ayyukan da wadansu daga cikinsu suke yi a Najeriya, inda suke bata sunan kasarsu a idon duniya.”

Ya yi alkawarin isar da wannan sako ga jama’arsa da ba su samu halartar taron ba.