✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an Amurka sun je Turkiyya don matsa lamba ga Shugaba Erdogan

Mataimakin Shugaban Amurka, Mike Pence, a shekaranjiya Laraba ya jagoranci wani babban ayari zuwa Turkiyya, domin yin matsin lamba ga Shugaba Recep Tayyib Erdogan kan…

Mataimakin Shugaban Amurka, Mike Pence, a shekaranjiya Laraba ya jagoranci wani babban ayari zuwa Turkiyya, domin yin matsin lamba ga Shugaba Recep Tayyib Erdogan kan ya kawo karshen mamaye Arewacin kasar Syria da ya yi.

Shugaban Amurka Donald Trump ne ya tura wannan ayari, wanda ya ce ya kunshi Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo da nufin yin kira ga Turkiyya ya tsagaita wuta, yana mai cewa, akwai tsauraran matakai da Amurka za ta dauka a kan Turkiyya idan ba ta mika wuya ba, ciki har da matakin saka makudan kudaden haraji kan kayayyakin karafa da Turkiyyar ke shiga da su Amurka.

Tun bayan da ya ba da umarnin kaddamar da mamayar, Shugaba Erdogan, ya yi biris da kiraye-kirayen da kasashen duniya suke masa na ya janye dakarunsa, yana mai kafa hujja da cewa, so suke su kawar da duk ’yan ta’addan da suke kan iyakar kasarsa da Syria, abin da ya ce suna samun nasara.

Rasha za ta shiga tsakani

Kasar Rasha ta ce ba za ta bari yaki ya kaure tsakanin Turkiyya da Syria ba, yayin da Turkiyya ke ci gaba da kai hare-hare kan mayakan Kurdawa a Arewacin Syria.

A cewar wakilin Rasha na musamman a Syria Aledander Labrentyeb, Rasha ba za ta taba bari yaki ya barke a tsakanin kasashen biyu ba. Masu suka sun ce janye sojojin da Amurka ta yi ne ya ba wa Turkiyya damar cin karenta ba babbaka a yankin.

Rasha na daga cikin manyan kawayen Shugaban Syria Bashar al-Assad. A ziyarar da ya kai Hadaddiyar Daular Larabawa, Mista Labrentyeb ya ce Rasha ba za ta aminta da hare-haren da Turkiyya ke kaiwa ba.

Ya ce jami’an Turkiyya da na Rasha na kan tattaunawa kan lamarin. Dakarun Rasha da aka girke a Syria tun a shekarar 2015 har yanzu na rangadi a yankin.

Abin da ya faru kafin yanzu

Kwanaki tara da suka gabata ne Turkiyya ta kaddamar da hare-hare a Arewacin Syria da nufin kawar da mayakan Kurdawa da ake kira SDF daga yankin.

Dama Turkiyya na yi wa mayakan kallon ’yan ta’adda.

Haka ma gwamnatin Turkiyyar na son samar da sansani a yankin da nufin maido da ’yan Syria da a yanzu ke gudun hijira a kasarta.

To sai dai masu suka na zargin cewa wadanda Turkiyya ke kai wa harin fararen hula ne, inda suka yi gargadin cewa Turkiyya na kokarin aikata kisan kiyashi ne.

Alkaluman da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar sun nuna cewa an kashe gwamman fararen hula, kuma mutum dubu 160, sun tsere daga muhallansu.

A baya mayakan Kurdawa sun hada hannu da sojojin Amurka wurin fatattakar Kungiyar IS daga Syria. A yanzu kuma sun bayyana janye sojojin Amurka da Shugaba Trump ya yi a matsayin yaudara.

Ana kuma fargabar rikicin zai iya sanadiyyar sake bullar kungiyar IS a Syria.

Yanzu haka ana tsare da dubbai daga cikin tubabbun mayakan Kungiyar IS da iyalansu, kuma wasu rahotanni na cewa fadan ya yi sanadiyyar tserewar wadansu daga cikinsu.

Haka ma kungiyoyin agaji da dama sun dakatar da ayyukansu a yankin tare da kwashe ma’aikatansu.

Yayin da matsin lamba ya yi yawa, mayakan Kurdawa sun bayyana kulla yarjejeniyar hada-hannu da gwamnatin Syria wurin mayar wa Turkiyya martani.

Matakin da Amurka da sauran kasashen suka  dauka kan Turkiyya

Amurka ta sanar da saka takunkumi kan kadarorin ma’aikatun tsaro da makamashi da kuma harkokin cikin gida na Turkiyya, bayan matsin lamba kan gwamnatin Amurka daga ’yan majalisa.

Bugu da kari, Shugaba Trump ya sanar da karin haraji da kashi 50 tare da dakatar da yarjejeniyar Dala biliyan 100 da gwamnatinsa ke kan kullawa da Turkiyya.

Trump ya kuma rubuta a shafinsa na Twitter cewa “Amurka da kawayenta sun kubutar da Syria daga Kungiyar IS kuma ba za su sa ido Turkiyya ta ruguza wannan nasarar ba.’’

Shi ma Mataimakinsa Mike Pence ya ja kunnen Turkiyya da ta kwana da sanin cewa akwai karin takunkumi, idan har ba ta gaggauta tsagaita wuta ba tare da tattauna hanyar samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

A shekaranjiya Laraba Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya sake gudanar da zama don tattaunawa kan farmakin da dakarun Turkiyya ke kaddamarwa a Arewacin Syria, yayin da Shugaban Turkiya, Racep Tayyip Erdogan ke cewa, ba su da niyyar dakatar da wannan farmaki duk da matsin lambar da suke fuskanta daga kasashen duniya. Yanzu haka ana fargabar cewa, sakamakon wannan farmaki, akwai yiwuwar mayaka masu nasaba da Kungiyar ISIS su arce daga yankin.

A daidai lokacin da farmakin na Turkiya ke ci gaba da haddasa cece-ku-ce a sassan duniya, kasar Amurka ta ce, ba ta da masaniya game da tserewar mayakan ISIS daga fursunonin da dakarun Kurdawa ke tsare da su.

Wannan na zuwa ne bayan rahotanni sun ce, hare-haren Turkiyya sun yi sanadiyar tserewar ’ya’yan Kungiyar ISIS masu hadarin gaske.

A bangare guda, kasashen Birtaniya da Spain sun bi sahun manyan kasashen duniya wajen dakatar da sayar wa Turkiyya makamai saboda wannan farmakin da take kaiwa.

Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Dominic Raab ya ce, daga yanzu ba za su bayar da lasisin shigar da makamai cikin Turkiyya ba wanda za a iya amfani da su a Syria, yayin da kasar Spain da ke kan gaba wajen sayar wa Turkiyyar makamai, ta sanar da daukar irin wannan mataki.

Sai dai Turkiyyar ta yi watsi da matakin da kasashen duniya suka dauka na juya mata baya, tana mai cewa za ta ci gaba da aikinta na kakkabe duk wata kungiyar ’yan ta’adda da suka hada da mayakan ISIS a Syria.

Trump ya shaida wa manema labarai a fadarsa da ke Washington cewa, zai yi kokarin samar da hanyar tsagaita wuta a farmakin na Turkiyya, kuma saboda haka ne ya bayar da umarnin sanya wa kasar takunkumi.

Kazalika Shugaban Rasha Bladimir Putin ya gayyaci Erdogan zuwa birnin Mosko don tattaunawa game da wannan rikici. Sanarwar da fadar Keremlin ta fitar a safiyar shekaranjiya Laraba, ta ce, nan ba da jimawa ba ne Erdogan zai isa birnin na Mosko bayan da shugabannin biyu suka yi tattaunawa ta tarho a tsakaninsu.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi biris da kiran tsagaita luguden wuta a Arewacin Siriyar, har sai kasar ta kakkabe gungun ’yan ta’adda da suka yi kaka-gida a yankin iyakar kasar Turkiyya da Siriya.

A cewar Shugaba Erdogan,Turkiyya za ta ci gaba da kai hare-hare har sai ta cimma burinta a yankin. Ya yi bayani cikin harshen Turkanci cewa, “Mun kawar da duk ’yan ta’addan da ke garin Jarabulus, shin Turkawa sun yi kama-wuri-zauna a garin? A’a, ’yan asalin garin ne kawai a wurin.”

Erdogan ya bayyana wadanda ya ce  ba su son farmaki a tafkin zaman lafiya inda ya ce “Wadanda ba su ganin alburusan da kungiyoyin ta’addanci ke harbawa zuwa kasarmu su ne masu kira a dakatar da farmakin tafkin zaman lafiya.”

 

Rahotanni daga BBC da BOA