Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Jami’an kula da motocin sufuri sun kashe mai talla da duka a Kalaba

Micheal bayan

Wasu jami’an da Gwamnatin jihar Kuros Ribas ta kaddamar don lura da motocin sufuri na gwamnati (DOPT) sun kama wasu matasa biyu masu talla inda suka rufe su da duka har sai da suka mutu a safiyar yau Juma’a kusa da Ofishin tura wasiku da ke Kalaba babban birnin jihar.

Daya daga cikin wanda aka kashe mai suna Michael, mahaifin ‘ya’ya biyar ne kafin jami’an su kashe shi sai da ya rika rokon su akan laifin da ya aikata, amma duk da haka suka sauka a motar su kirar Hilux suka rufe shi da duka, hakan ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

ADVERTISEMENT

Wasu fusatattun matasa sun kai gawar Michael, ofishin Gwamnan jihar kusa da ofishin jami’an da suka yi kisan don nunawa gwamnantin jihar rashin amincewarsu akan yadda ake kuntatawa jama’ar jihar.

ADVERTISEMENT