Jami’an kwastan masu kula da bakin iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin sun bukaci a kammala aikin sabunta bakin iyakar da ke tafiyar hawainiya, yau shekaru biyu ke nan da aka ba da shi, kuma sun ce wannan na kawo wa aikinsu cikas.
Da yake wa taron manema labarai jawabi, shugaban kwastam mai kula da bakin iyakar, Kwanturola Othman Suleman ya ce rashin wadatattun ofisoshi yana shafar aikinsu, kodayake hakan bai sa sun gaza wajen gudanar da ayyukan nasu ba.
Kwanturola Othman ya ce kudin shigar da suka samu daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu ya fi abin da suka samu a bara gaba daya. “Samun nasarar hakan ya biyo bayan irin goyon bayan da muke samu daga Kwanturola-Janar Abdullahi Dikko Inde da mukarabansa, wanda ba don haka ba da Najeriya ta rika babbar asarar kudin shiga”. Inji shi.
Da ya tabo dangantakar hukumar kwastan da sauran jami’an tsaro da ke aiki bakin iyakar ta jamhuriyar Benin da Najeriya, sai ya ce dangantakar mai karfi ce domin kowane wata suna ganawa tsakaninsu don kara samar da dabarun gudanar da ayyukansu da hanyoyin inganta su, musammam ma kan yadda za su dakile shigo da makamai ko kuma duk wani mugun abu da zai cutar da kasa.
Ya ce suna ta kokarin samar da kyakkyawar dangantarsu da jami’an tsaro na kasar Benin yadda za a gudanar da aiki kowace kasa ta amfana, musamman a fannin lamarin da ya shafi karuwar samun kudin shiga, hasali ma ga shi an samar musu sabuwar na’ura mai binciken kwakwaf na manyan motoci.
Daga karshe ya yi fatar aikin bakin iyakar zai kammalu cikin lokaci ta yadda za su ci gaba da jin dadin gudanar da aikinsu.
Jami’an kwastam sun bukaci a kammala aikin bakin iyaka
Jami’an kwastan masu kula da bakin iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin sun bukaci a kammala aikin sabunta bakin iyakar da ke tafiyar hawainiya, yau shekaru …