✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro su cire hannunsu daga sana’ar kifi – Mu’azu Isah

Kasuwancin kifi yana da mahimmanci, kuma  an shafe shekara da shekaru ana kasuwancinsa daga garin Maiduguri zuwa sauran sassan Najeriya da makwabtan kasashe.  Sai dai…

Kasuwancin kifi yana da mahimmanci, kuma  an shafe shekara da shekaru ana kasuwancinsa daga garin Maiduguri zuwa sauran sassan Najeriya da makwabtan kasashe.  Sai dai kasuwancin kifin ya gamu da cikas dalilin rikicin Boko Haram.  Yanzu haka jami’an tsaro ne ke gudanar da wannan harka idan kana so ka yi kasuwancin kifi, sai dai ka nemi jami’an tsaro wannan ya sa Aminiya ta tattauna da Sakataren Kungiyar ’Yan Kifi da ke Tashar Baga a Maiduguri, Mu’azu Isah Mado inda ya ce suna so jami’an tsaro su cire hannu daga harkar:

Yaya harkar kasuwanci kifi take a yanzu ganin kalubalen da harkar take fuskanta tun fara rikicin Boko Haram?

To a gaskiya kasuwancin kifi da aka san ta sama da shekara 50 a baya a nan Borno ta mutu, idan aka yi la’akari da shekarun baya. Duk da cewa sha’anin tsaro daidai gwargwado ya samu, amma a gaskiya mu masu sayar da kifi  ba mu samu sauki ba don kullum abin sake lalacewa yake yi, ba a kawowa daga garin Baga. A yanzu duk abin ya tsaya cak babu wani kasuwancin kifi da ake yi kamar da.

Abin da yake ba mu mamaki shi ne daukacin hadin gwiwar jami’an tsaro, sun ce ba za a kawo kifi daga Tafkin Chadi ba, kuma ba za a kawo kifi daga garin Baga ba, saboda suna da alaka da Boko Haram, to amma kuma sun bari ana daukar kifin a tafi da shi Adamawa da Jigawa a je a sayar. Amma mu a nan Borno an hana mu. Ga shi kuma ana kaiwa wasu wurare, to abin da ya kamata idan za a hana sai a hana gaba daya, idan kuma za a sayar ne to a bari a sayar gaba daya.

Ina gaskiyar cewa jami’an tsaro na kasuwancin kifi da shanu a yankunan da suka hana ku?

A wani bangaren za ka iya cewa akwai kanshin gaskiya, ka ga matsalar da take faruwa su manyan jami’an tsaron ba za su san mene ne yake tafiya ba, amma kananan da suke kan hanya, kuma su suke yaki, yanzun za mu iya cewa kasuwancin ma su suke yi, don garin Baga babu mutane sai su Jami’an tsaron  su da ’yan Boko Haram a can to abin tambaya a nan shi ne ta ina ne kifi yake zuwa, kuma wa yake kamun kifin? To ka ga a nan ne za ka tsaya ka yi tunani wa ke kamun kifi, idan ba su ba, don babu ta inda kifi zai shigo Maiduguri sai ta wannan bangare, kuma ba a Baga ne kawai ake samun kifi ba, akwai kifi a cikin kasar Chadi, har a kasar Sudan to kuma wacancan wuraren babu Boko Haram a bar mutanenmu su je su sayo a can su kawo shi nan Maiduguri mana. Za a biya masa duk wata tara ta ka’ida da ake caji a kan hanyar wadancan kasashe, sannan ka zo ka biya na Najeriya to amma in ya shigo cikin Borno sai a ce wai ka dauko kayan Boko Haram, to amma kuma za a bar shi a kai Jihar Adamawa a sayar. To wannan abin shi ke daure mana kai, ya kamata jami’an tsaro su gane cewa ko muna yaki da Boko Haram to dole ne fa sai mun yi yaki da talauci, ba zai yiwu a ce muna yakar Boko Haram kuma duk matasanmu suna cikin talauci ba. Sanin kowa ne cewa matasa idan ba za su samu aikin yi ba, a ko’ina ne dole ba zaman lafiya don wata rana motar da za ka hau ma za su kwace, to dole ne sai an yi la’akari da wadannan abubuwa.

Gwamna Babagana Umara ya gana da Babban Hafsan Sojin Najeriya, inda ya roki a bude kasuwar kifi, yaya kuka ji?

Alhamdulillahi shi Gwamna ya lura da  halin matsin  da muke ciki ne ya kai shi ga roka, mun gode masa. Abin da yake hannun jami’an tsaro Gwamna ma kawai sai dai ya roka, ya yi kokari da ya yi rokon, amma har yanzu muna sauraro dai ba mu ga wani abu a aikace ba. Maimakon haka ma sai muka ga wani tsanani ya sake zuwa mana fiye da na da, domin kuwa ko kifi da ake zuwa da shi a da kwali daya kwali biyu yanzu kamawa ake yi. Muna ganin abin ya samu sauki, amma  daga yin rokon zuwa yau kifin ma babu shi a Tashar Baga.

Wacce hujja suke bayarwa kan dalilin kama kifin?

Ba su ba da wata hujja illa su ce maka kawai kayan Boko Haram ne.

Akwai kwamitin duba lamarin da Gwamnatin Jihar ta kafa don samun dai-daito ina aka kwana?

Gwamna ya kafa wani kwamiti na farfado da kasuwanci a Jihar Borno, to an bukaci mu bayar da koke-kokenmu da shawarwari, alhamdulillahi mun riga mun mika namu koke-koken da shawarwari a rubuce, kuma muna fatar samun ci gaba daga inda ake.  Shi ma Gwamnan ya yi kokari wajen farfado da harkar kasuwanci a jihar musammam a nan Maiduguri.

A kungiyance kun taba zama da manyan shugabannin sojoji don gabatar musu da koke-kokenku?

Ka san matsalar aikin soja, mun zauna da wakilan Janar Buratai, duk wani Kwamandan Rundunar  Operation Lafiya Dole da aka kawo mun zauna da shi, kuma mun sha zama da duk wani Kwamandan Runduna ta 7 da aka kawo mun gabatar musu da koke-kokenmu a rubuce. Janar Buratai ya san matsalolinmu, yau kusan shekara 4 ke nan muna jiran yadda za a magance mana.Wallahi mu masu kasuwancin kifi a yanzu muna cikin wani mawuyacin hali na rashin gudanar da sana’armu da karayar tattalin arziki duk mun durkushe, misalin mutumin da a da yake da jarin Naira miliyan 50 a yanzu ba ya da Naira dubu 100.

Shin rikicin Boko Haram ya shafi ’ya’yan kungiyarka?

Ai duk garin nan mu ne ya fi shafarmu, idan ka lura gaba daya sana’ar kifin ana yin ta ce a Tafkin Chadi to yanzu Boko Haram sun tare a can. Ka ga mutanenmu sun baro sana’arsu sun baro gidajensu sun baro iyalansu da sauran wasu abubuwansu, a yayin da kuma aka kashe wadansu. Ko a nan Maiduguri mun yi asarar ’yan kungiya ba  adadi, ko a nan Tashar Baga akwai mutanenmu da aka kashe masu rajisata ma kawai za su kai fiye da 300 wadanda aka kashe ban da wadanda ba su da rajista. Kuma ina tabbatar maka an yi asarar dukiya da ta fi ta Naira biliyan biyu a bangrenmu na ’yan kifi.

A karshe wane kira kake da shi ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Borno don ganin an farfado da kasuwancin kifin?

Rokona ga Gwamnatin Tarayya shi ne ta dubi wannan lamari namu na Kasuwar Kifi ta agaza mana ta sanya baki a bude mana kasuwar don abu ne da yake da muhimmanci ga tattalin arziki da samar wa matasa aikin yi. Idan aka bai wa harkar kasuwancin kifi muhimmanci za ta samar wa matasa sama da dubu 50 aikin yi. Don haka muke rokon Gwamnatin Tarayya ta duba ta tallafa mana ta yadda za a ceci rayuwarmu kuma a farfado da tattalin arzikin kasa.