Da Dumi Dumi

Jami’an tsaro sun yi awon gaba da Naziru Sarkin Waka

A daren jiya Laraba Jami’an tsaro sun yi awon gaba da Naziru Sarkin Waka, kuma zuwa yanzu ba asan wajen da aka kai shi ba, kamar yadda wata kafar yada labarai ta ‘yan Kannywood ta dandalin sada zumunta da ake kira HausaFilms Alieve ta bayyana.

Kafar ta shaida cewa an yi awan gaba da shahararren mawakin ne bayan nuna masa takardar umarnin kotu wanda aka bada izini cafke shi.

Share