✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaron sun kama masu garkuwa da mutane 9 a jihar Kogi

Jami’an tsaron farin kaya sibil defens NSCDC, rashen Jihar Kogi, sun gabatar da wasu mutane 9 ga manema labarai, wadanda ta ce masu aikata miyagun…

Jami’an tsaron farin kaya sibil defens NSCDC, rashen Jihar Kogi, sun gabatar da wasu mutane 9 ga manema labarai, wadanda ta ce masu aikata miyagun laifukan da suka hada da yin garkuwa da mutane da sace-sace da kuma sauran ayyukan ashsha.

Kwamandan rundunar a Jihar ta Kogin, Olusola Philip Ayodele, wanda ya gabatar da mutanen ga manema labarai, ya ce an yi nasarar kame su ne ta hanyar bayanan sirri da Hukumar ta samu.

Ya ce, biyu daga wadanda ake zargin, Usman Mohammed Sanni da kuma abubakar Musa, sune suka yi garkuwa da wata mata mai suna Binta Haruna a gidanta da ke Jida Bassa a yankin Karamar Hukumar Ajaokuta; amma an gano su tare da cafke su a wani wuri cikin jihar Neja.