Da Dumi Dumi

Jami’ar ABU ta samar da sabon irin wake mai jure kwari

Farfesa Mohammad Fuguci Isyaku a yayin da yake bayanin sabon irin wake da Cibiyar Binciken ta IAR ta samar
Farfesa Mohammad Fuguci Isyaku a yayin da yake bayanin sabon irin wake da Cibiyar Binciken ta IAR ta samar

Shugaban Sashin Binciken irin na Cibiyar Nazarin Aikin Gona (IAR) ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya,  Farfesa Mohammad Fuguci Isyaku, ya ce sun samar da wani irin wake mai juriya ga kwari.

Farfesa Mohammad Fuguci, ya bayyana haka ne lokacin taron manema labarai da aka gudanar a cibiyar da ke Zariya, inda ya ce cibiyar ta samar da sabon irin waken ne domin Najeriya ta samu karin kudin shiga da ya kai Naira biliyan 48 a duk shekara.

Farfesa Fuguci Isyaku ya ce cibiyar ta IAR da ke Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ta shafe sama da shekara 10 tana bincike a kan yadda za ta gano hanyar magace kwarin da suke addabar gonakin wake a kasar nan.

A cewarsa, wadannan kwari suna janyo wa manoma hasarar akalla kashi 80 na waken da suke shukawa.

Ya ce masana kimiyyar tsirrai ne suka hadu domin samar da sabon irin waken da zai kare kansa daga wadannan miyagun kwari.

ADVERTISEMENT

Farfesa Fuguci Isyaku ya ce sakamakon samar da irin waken,  manoma za su shuka waken ba tare da sun yi masa feshi mai yawa kamar yadda suka saba yi a baya ba,

Ya kara da cewa, maimakon yin feshin magani sau shida zuwa takwas da manomi ke yi a yanzu bai wuce ya yi feshin magani sau biyu ba, kuma zai samar da amfani kamar an yi mai feshin sau shida zuwa takwas.

Farfesan, ya kuma ce a sanadiyar wannan garabasa sun yi  hasashen cewa Najeriya za ta iya amfana ta wajen samun kudin shiga har Naira biliyan 16 ta hayar rage amfani da maganin kwari. Na biyu kuma wannan irin yana da amfani a jikinsa wanda ya kai kashi daya daga cikin biyar  na sauran amfani.

Masanin ya ce wannan wata sabuwar dabara ce na zamani a kimiyance wadda a ciki ake bukatar duk kasashen duniya sai sun nuna alama cewa shi wannan irin waken da aka bullo da shi ta wannan hanya ta cika duk wasu sharuddan da ake bukata na kasancewarsa ya zama abinci ne kuma ba ya cutar da muhalli.

Ya ce suna fata manoma da masu cin wake za su rungumi wannan dabara, kuma ya ce kowace kasa tana alfahari ne da ilimi da hazakar da masananta ke bullowa da shi a koyaushe domin su warware wa kasar matsalolin da suke addabarta.

Ya kara da cewa kada mutane su rudu da masu kokarin dulmiyar da jama’a cewa an hana su fahimtar ci gaba da ake da shi ko ake kawowa a cikin kasa na fasahohin zamani, don haka su yi kokarin rungumarsu domin ci gabansu .

“Wannan sabon irin mun bai wa manoma, kuma sun jarraba shi, tare da nuna gamsuwarsu ta hanyar yin sa da wuri, da kuma samu amfani mai yawa da ma rage amfani da maganin kwari wanda manomin wake ya sani cewa yana daya daga cikin babban nauyin da manomi ke sha wajen noman wake,” inji shi.

Farfesan ya ce “Ina fata mutane za su goya mana baya wajen rungumar wannan sabon iri don mu ci gaba da biyan bukatun manoma a Najeriya, abinci ya wadata, kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ke cewa noma na daya daga cikin abin da kasarmu za ta kwato kanta daga tarkon  dogaro da man fetur, da ba ya da tabbas wajen samar wa kasar nan kudin shiga.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya