✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Al-Nahda da ke Nijar ta ba Usman Sarki digirin dokta a kasuwanci 

Alhaji Muhammadu Usman Sarki yana daya daga cikin matasan ’yan kasuwa a Jihar Katsina wanda wata jami’a a Jamhuriyar Nijar ta bai wa digirin girmamawa…

Alhaji Muhammadu Usman Sarki yana daya daga cikin matasan ’yan kasuwa a Jihar Katsina wanda wata jami’a a Jamhuriyar Nijar ta bai wa digirin girmamawa na Dokta a kan Harkokin Kasuwaci a kwanakin baya.

Shi ne matashin dan kasuwa na farko a tarihin jihar da ya samu irin wannan karramawa daga wajen kasa ta fuskar kasuwanci.

Aminiya ta nemi jin ta bakinsa kan dalilin da yake gani ya sanya jami’ar mai suna Al-Nahda da ke birnin Yamai ta ba shi wannan matsayi inda ya ce, “A tunanina bai wuce yadda nake kokarin ganin cewa harkokin kasuwanci sun bunkasa a tsakanin wadannan kasashe biyu ba. Da kuma hana matasa zaman kashe wando ta hanyar bullo da wasu masana’antu da kamfanoni domin samar da abin yi ga al’umma. Wannan ina jin su ne dalilan da suka sanya wannan jami’a ta yi bincike a kaina domin irin kyakyawar alakar da muke da ita da mutanen Nijar musamman ta fuskar kasuwanci. Na yi mamaki lokacin da aka fada min cewa za a ba ni wannan digiri na girmamawa, sai kuma al’amarin Allah abin ba zai zamo abin mamaki musamman idan duk abin da mutun yake yi yana sa tsoron Allah a ciki.”

A kan batun kafa wata kungiya mai karfi ta fuskar kasuwanci a tsakanin kasashen biyu da wani shugaban ’yan kasuwa da ke Jihar Damagaram mai suna Alhaji Dan Feti ya kawo shawara, Dokta Muhammadu Sarki ya ce yin haka wani ci gaba ne a tsakanin kasashen Afirka baki daya, “Samun hadaddiyar kungiya a wannan harka zai kara daga martabar kasashennmu, zai kuma kara daga darajar kasuwancinmu da kullum ke fuskantar barazana daga kasashen da suka ci gaba. A yanzu harkar kasuwanci ke tafiyar da duniyar baki daya. Kasar China ta ishe mu misali. Kazalika samar da kungiyar zai kara taimakawa wajen tsayar da daidaitaccen farashi maimakon kwan-gaba-kwan-baya da ake samu a harkokin kasuwancinmu. Muna da albarkatu bila adadin a cikin kasashenmu, amma muna kallo wadansu su zo suna amfani da su mu kuwa muna zama ’yan kallo. To yanzu wannan lokaci ya wuce. Za mu yi iya kokarinmu mu ga muna gogayya da kowace kasa ta fuskar kasuwanci,” inji shi.

Da ya juya ga gwamanti, Dokta Sarki ya yi kira ta shigo cikin harkokin kasuwanci gadan-gadan ta hanyar tallafa wa ’yan kasuwar, koda ta hanyar sayen kayayyaki daga wajensu kai-tsaye ko kuma sayowa ta hanyarsu. Sannan ya nemi a rika ba ’yan kasuwar filayen da za su rika kafa masana’antunsu da kuma shirya musu taron kara wa juna sani ta fuskar kasuwanci inda za a gayyato masana domin bayar da lacca. Sannan ta rika tallafa wa masu kananan sana’o’i da jari domin ta haka ne za su girma. Kuma ta rika kara wa duk wanda ya fito da wata fasaha kwarin gwiwa domin ta haka ne sauran kasashe suka ci gaba.

Sai ya ja hankalin ’yan kasuwa  su rika hakuri da kowace irin riba suke samu ta hanyar saukaka wa al’umma tare da sanya farashi mai sauki ga kayan kasuwancinsu. Su kuma masu saye su rika lura da yanayin da ake shiga musamman na karanci da hawa da sauka da canjin kudi ke yi. Sai ya kara jan hankalin matasa su kara jajircewa wajen gudanar da harkokin kasuwanci da sana’o’in hannu, “Kada mutum ya ce don ya yi ilimi babu abin da zai yi sai aikin gwamnati. Shin ina ayyukan suke a yanzu? Mutum nawa ke zaman jira kafin kai? Amfanin ilimi yin aiki da shi, saboda haka yi amfani da shi don fito da wani abu na ci gaba,” inji Dokta Sarki.