✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Bingham za ta hada kai da ‘yan jarida don inganta aikinsu

Hukumar Gudanarwar Jami’ar Bingham  da ke Kadope a Karamar Hukumar Karu Jihar Nasarawa ta sha alwashin hada kai da dukka kafofin yada labarai a jihar…

Hukumar Gudanarwar Jami’ar Bingham  da ke Kadope a Karamar Hukumar Karu Jihar Nasarawa ta sha alwashin hada kai da dukka kafofin yada labarai a jihar wajen yada labarum jami’ar da jihar baki daya yadda ya dace.

Shugaban Jami’ar Farfesa William Kurid ne ya bayyana haka a jawabinsa, lokacin da yake karbar bakuncin mambobin kungiyar masu aiko da rahotanni ta kasa reshen jihar wadanda suka kai wata ziyara ta musamman jami’ar a karshen makon jiya.

Ya ce ba shakka ’yan jarida a jihar da kasa baki daya suna bada gagarumin gudumawa wajen ci gaban jami’ar da kasa baki daya; saboda haka ya zamowa jami’ar dole ta hada kai da su a wannan bangare. A cewarsa, hadin gwiwar zai taka muhimmiyar rawa musamman wajen yaki da ayyukan ’yan jarida na bogi masu yada labarun kanzon kurege a yanar gizo, wanda ya ce ya zama ruwan dare a kasar nan.

Ya ci gaba da bayyana cewa, “a gaskiya kuna ba da gagarumin gudumawa wajen yaki da labaran karya, musamman ta bayyana wa al’umma gaskiyar lamarin dangane da ayyukan jami’ar nan da kasa baki daya. Haka zalika ku kan jawo hankulanmu kan kura-kuranmu wanda hakan kan taimaka mana wajen yin gyara a kansu. Saboda haka ba shakka kuna taimaka mana sosai. hakan ya sa tuni muka yanke shawarar barin kofarmu a bude wa dukka ‘yan jarida a jihar nan da kasa baki daya; inda za mu rika ba su cikakken bayanai da suke so dangane da ayyukan jami’ar nan a kowane lokaci,” inji shi.

Shugaban jami’ar ya kuma yi amfani da damar inda ya sanar cewa tuni jami’ar ta fara aiwatar da wasu kwasa-kwasanta na cikin gida da ta kirkiro don daukaka sana’oin hannu don bai wa dalibanta damar dogara da kansu idan suka kammala karatu. Wadannan kwasa-kwasan sana’oin hannun, a cewarsa, sun hada da na kafinta da tela da walda da gyaran rediyo da rini da sauransu.  Sannan ya shawarci iyaye su turo ‘ya’yansu su koyi sana’oin don amfanarsu da al’umma baki daya.

Tun farko a jawabinsa, Shugaban Kungiyar ’yan jarida masu aiko da rahotanni ta kasa reshin jihar, Mista Isaac Upkoju, ya ce makasudin ziyarar shi ne hada zumunci da neman yin aiki tare da jami’ar a yayin gudanar da ayyukan kungiyar na nemo tare da yada labarun jami’ar da jihar baki daya. Ya ce ba shakka jami’ar ta samu gagarumin ci gaba a karkashin jagorancin shugabanta na yanzu, musamman a bangarorin gine-gine da ingantaccen yanayin ilimi da sabbin kwasa-kwasanta, wadanda ya ce suna taimakawa wajen kawo canji mai ma’ana a fannin ci gaban ilimin jihar da kasa baki daya. Sannan ya tabbatar masa cewa a nasu bangaren ‘yan jarida a jihar za su ci gaba da yin aiki tare da jami’ar wajen cimma burin samun ingantaccen ilimi a jihar.

A yayin ziyarar, mahukuntan jami’ar sun zagaya da ‘yan jaridar, inda suka ganewa idanunsu wasu daga cikin ayyukan daukaka ilimi da jami’ar ke aiwatar wa; da suka hada da sabbin dakunan karatu da daukar darasi da gidan rediyon makarantar da asibitocin zamani na dalibanta da dai sauransu.