✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyar APC ce za ta lashe zabe mai zuwa – Tuggar

Wani jigo a Jam’iyyar APC Alhaji Yusuf Maitama Tuggar ya ce akwai yiwuwar samun nasarar jam’iyyar a zabubbuka masu zuwa a shekarar 2015, musamman ganin…

Wani jigo a Jam’iyyar APC Alhaji Yusuf Maitama Tuggar ya ce akwai yiwuwar samun nasarar jam’iyyar a zabubbuka masu zuwa a shekarar 2015, musamman ganin yadda Jam’iyyar PDP ta gaza cimma muradun jama’ar kasar nan. Alhaji Maitama Tuggar ya ce a zaben da ya wuce da karfi aka dora PDP a mulkin jihar don haka jami’an tsaro su nisantar da kansu wajen cin zarafin mutane a wannan siyasa da ake ciki don tabbatar da zaman lafiya a Najeriya. Ya ce APC ta fara rajistar magoya kuma za ta gudanar da zaben shugabannin da suka dace don jan ragamarta, kuma duk mai son wata kujera sai ya shiga zaben fidda gwani tare da yin abin da ya dace don zabar mutanen kirki a zabe mai zuwa. Ya ce abin da ya fi tsayawa a ransa shi ne yadda za a yaki talauci da inganta albarkatun da Allah ya hore wa Jihar Bauci da kuma samar da tsarin noma irin na zamani domin ci gaban jama’ar jihar.