Daily Trust Aminiya - Jam’iyyar APC ta gudanar da taron dinke baraka a Jihar Gombe
Subscribe

Jam’iyyar APC ta gudanar da taron dinke baraka a Jihar Gombe

A ranar Talatar da ta gabata ne Jam’iyyar APC reshen Jihar Gombe a karkashin jagorancin tsohon shugaban Jam’iyyar CPC na Jihar Alhaji Sulaiman Hassan Jara ta gudanar da taron dinke barakar da ke tsakanin ’ya’yanta a jihar musamman dan Majalisar Tarayy Alhaji Khamisu Mailantarki da tsohon dan takarar Gwamna a CPC Alhaji Abubakar Aliyu.
A wurin taron Alhaji Abubakar Aliyu, ya ce musanta zargin cewa tsohon Gwamnan Jihar Alhaji danjuma Goje, kuma jagoran jam’iyyar ya saye shi.
Game da zaben shugabannin jam’iyyar bayan karewar wa’adin shugabanin riko Abubakar Aliyu ya ce sai cikakken dan APC ne za a ba damar takara ba kamar yadda a baya Sanata Goje ya yi babakere wajen dauko ’ya’yan sabuwar PDP ya dora su ba. Ya ce ‘yan asalin jam’iyyun nan uku da aka yi hada ka da su ne za su yi takara, ko dan sabuwar PDP zai shigo sai wadannan sun shiga tukuna.
Wani Dattijo a tafiyar APC Alhaji Jauro Tela (J.T) cewa ya yi tunda yanzu jam’iyyarsu ta APC ce babbar jam’iyyar adawa abin da ya rage musu shi ne su tashi tsaye don kwace mulki daga hannun PDP a zaben 2015, saboda PDP ba alheri ba ne.
Ya shawarci shugabannin Jam’iyyar APC cewa lokaci ya wuce da za a tsaya ana fada da Sanata danjuma Goje, abin yi kawai shi ne a zauna a yi sulhu tunda doka ta nuna shi ne jagoran jam’iyyar a jihar.
Alhaji Magaji Kwairanga da Magaji Baba, shawartar iyayen jam’iyyar suka yi cewa ya dace a kafa kwamitin ya dattawa a yi zama da Sanata Goje a Gombe ko a bi shi Abuja don a samu masalaha wajen yi wa kowane bangare adalci.

texem
More Stories