✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyar APC ta yi taron goyon bayan takarar Kwamared Sabo

Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi ta yi gangamin nuna goyon baya ga wani tsohon malamin jami’a Kwamared Sabo Mohammed domin tsayawa takarar dan Majalisar Wakilai…

Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi ta yi gangamin nuna goyon baya ga wani tsohon malamin jami’a Kwamared Sabo Mohammed domin tsayawa takarar dan Majalisar Wakilai daga Bauchi, saboda irin goyon baya da dogewarsa cikin harkokin siyasa da nufin kawo sauyi. Jigo a APC kuma tsohon Ministan ’Yan sanda Dokta Ibrahim Yakubu Lame ya yaba rawar da Kwamared Sabo ke takawa da nufin ciyar da harkokin siyasa gaba bisa tafarki na gaskiya. Ya bukaci ’ya’yan jam’iyyar da sauran jama’a su zauna da shirin kawo sauyi a siyasa mai zuwa ta hanyar fito da shugabanni na kwarai da jama’a ke so. Ya gargadi magoya bayan jam’iyyar su nisanci siyasar kage da yarfe ko cin zarafin juna, su tsaya kan akida ta kawo sauyi mai amfani da za ta taimaki kasa da jama’a wajen inganta rayuwarsu ba tare da sace dukiyar kasa ko nuna halin jari-hujja ba. Kwamared Sabo Mohammed ya ce ya sake nuna sha’awarsa ce ta takarar saboda irin goyon bayan da mutane ke bas hi wajen ganin ya sake fitowa, musamman saboda ganin cancantarsa da kwarewarsa na tsohon malamin jami’a wanda ya jima yana gudanar da harkokin siyasa don kawo sauyi daga irin mawuyacin halin da ake ciki a kasar nan. Ya shawarci ’yan siyasa su kasance masu akidar ciyar da kasa gaba ta hanyar samar da wakilan da za su taimaka wajen ci gaban yankunansu ba tare da warwashe dukiyar jama’ar kasa kamar yadda ke faruwa a wannan lokaci ba.