✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Jam’iyyar APC za ta kai al’ummar kasa tudun tsira’

Gwamna Ibrahim Gaidam na Jihar Yobe ya bayyana sabuwar jam’iyyar APC a matsayin jam’iyyar da za ta kai al’ummar kasar nan ga tudun tsira, su…

Gwamna Ibrahim Gaidam na Jihar Yobe ya bayyana sabuwar jam’iyyar APC a matsayin jam’iyyar da za ta kai al’ummar kasar nan ga tudun tsira, su fita daga halin rashin tabbas da suke ciki, musamman kan abin da ya shafi tabarbarewar harkokin tsaro da ma sauran harkokin rayuwar yau da kullum.
Bayanin haka kuwa yana kunshe ne a cikin wata takardar sanarwar da mai ba gwamnan shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Alhaji Abdullahi  Bego ya sanya wa hannu a gidan gwamnati da ke Damaturu.
Gwamna Gaidam ya ce nan ba da dadewa ba al’ummar kasar nan za su sami sa’ida daga kuncin rayuwar da suka dade a cikinta, inda mahukuntan jam’iyya mai jagorancin kasa suke gasa musu aya a hannu, domin yanzu an sami sabuwar jam’iyyar mai ceton al’umma ta APC.
Don haka ya taya sabuwar jam’iyyar ta APC murna saboda rijista da hukumar zabe ta yi mata da ma dukkan al’ummar kasa kan wannan abin farin ciki. Ya yi addu’ar Allah Ya sa samuwar hakan ta tabbata ta kasance silar samun ’yancin talakawa, domin matsayin tsarin dimokuradiyya zai samu muhallin da ya dace da shi.