✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyar Musulunci ta JCP ta matsa wa firayiministan Libya ya sauka daga mukaminsa

kungiyar ’yan uwa Musulmi ta Libya ta bukaci Firayiminista Ali Zeidan ya yi murabus, inda suka zarge shi da nuna gazawa wajen shawo kan cin…

Firayiministan Libya, Ali Zeidankungiyar ’yan uwa Musulmi ta Libya ta bukaci Firayiminista Ali Zeidan ya yi murabus, inda suka zarge shi da nuna gazawa wajen shawo kan cin hanci da rashawa da kuma kafa sojoji kasa a karkashin inuwa guda, sabanin gasa da adawar da ke tsakanin kabilu.
Mohammad Sawan, Shugaban kungiyar Musulunci ta JCP, wadda ita ce babbar jam’iyya mafi rinjaye a Majalisar Libya, ta bayyana cewa jam’iyyar na duba yiwuwar janye ministocinta biyar daga Gwamnatin Zeidan, wadanda suka hada da na man fetur.
Zeidan dai an zabe shi ne a matsayin Firayiminista cikin watan Oktoban bara, bisa la’akari da sassaukan ra’ayinsa. A halin yanzu yana fama da matsin lamba daga masu ra’ayin Musulunci da kungiyoyi masu cin gashin kansu, wadanda ba su gamsu da yadda yake kokarin shawo kan ma’aikatan hakar mai da ke yajin aiki a kasar, da kuma sojojin da suka yi rugu-rugu da harkar hako mai a kasar, al’amari da ke haifar musu da asarar biliyoyin dala.
Rikicin siyasa da matsalar tsaro ta baibaye kasar, da matsalar wutar lantarki da karancin rowan sha, inda mafi yawan Libiyawa ke kara shiga halin kunci tun bayan da aka kawar da Gwamnatin Marigayi Mu’ammar Gaddhafi.
Sawan dai yana zargi Firayimkinista Zeidan da yin almubazzaranci da kasafin kudin Libiya.