Da Dumi Dumi

Jam’iyyar PDP ba ta da wata matsala a Jihar Filato -Shabiri Danmama

Mataimakin sakataren kudi na jam’iyyar PDP reshen jihar Filato, Honarabul Shabiri Kabila John Danmama, ya bayyana cewa jam’iyyarsu ta PDP ba ta da wata matsala a Jihar Filato. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce dukkan masu cewa jam’iyyar PDP tana da matsala a Jihar Filato, irin mutanen nan ne da suka gudu suka bar jam’iyyar.
Ya ce a Jihar Filato  babu abin da za a cewa jam’iyyar PDP da gwamnan
jihar Jonah Jang sai dai godiya kawai.
Shabiri ya yi bayanin cewa  idan aka dubi zango biyu da tsohon gwamman
jihar Joshua Dariye ya yi, za a ga bai yi komai na cigaba ba, sai raba wa mutane kudi  kawai.
“Amma tun daga lokacin da Gwamna  Jang ya zo zuwa yanzu, kowa ya ga irin ayyukan raya kasa da ya yi a Jihar Filato,” inji shi.
Ya ce sakamakon irin ayyukan raya kasa da gwamna Jang ya yi  a zango na farko yasa al’ummar jihar suka sake zabensa a zango na biyu.  Ya ce a wannan zango na biyu ma  ya ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa a jihar nan, kamar gina  hanyoyin mota da gyara asibitoci da makarantu da dai.
Don haka ya ce mu ba mu da wata damuwa ko fargaba a jam’iyyarmu ta PDP, musamman kan zabubbuka masu zuwa na shekara ta 2015.

Share