✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyar PDP ta lashe zaben cike-gurbi na Majalisar Wakilai a Zaki da Gamawa

’Yan takarar Jamiyyar PDP Alhaji Auwal Muhammad Jatau da Alhaji Ahmad Madaki Gololo ne suka lashe zaben cike gurbi da aka yi na Majalisar Wakilai…

’Yan takarar Jamiyyar PDP Alhaji Auwal Muhammad Jatau da Alhaji Ahmad Madaki Gololo ne suka lashe zaben cike gurbi da aka yi na Majalisar Wakilai daga mazabun Zaki da Gamawa da ke jihar Bauchi a ranar Asabar din da ta gabata.

Da yake bayyana sakamakon zaben jami’in tattara sakamakon zabe a Karamar Hukumar Zaki Farfesa Ahmed Kutama ya ce Auwal Jatau na Jam’iyyar PDP ya sami kuri’a dubu 15 da 405 inda ya doke abokin takararsa Alhaji Umar Tata na Jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’a dubu 15 da 307.

A mazabar Gamawa kuwa Baturen Zabe na Yankin Dokta Abubakar Mohammed na Jami’ar Tarayya da ke Dutse, ya ce Madaki  Gololo na Jam’iyyar PDP ya samu kuri’a dubu 21 da 223 inda ya doke abokin takararsa Isa Mohammed Wabu na Jamiyyar NNPP wanda ya samu kuri’a dubu 15 da 4.

Idan za a iya tunawa a watan Nuwamban bara ne Kotun Daukaka Kara da ke Jos ta soke zaben da aka yi wa Tata Umar na Jamiyyar APC a mazabar Zaki ta kuma soke zaben da aka yi wa Garba Gololo na Jam’iyyar APC sannan ta umurci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sake gudanar da zabubbuka a mazabun cikin kwana 90.

Da yake jawabi bayan da kammala zabubbukan Kwamishinan Zabe na Jihar Bauchi, Alhaji Ibrahim Abdullahi ya ce an yi zabubbukan cikin lumana kuma akwai ci gaba bisa yadda aka gudanar da zabubbukan bara.

An samu korafe-korafe na zargin tafka magudi da sayen kuri’u a lokutan zabubbukan, zargin da jami’an hukumomin zabe da na tsaro suka musanta.