✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyar PDP ta yi amfani da hotonan hanyoyin Laberiya don  bata Fashola

Jam’iyyar PDP ta yi amfani da hotonan wasu hanyoyi na kasar Laberiya, don maida martani ga Ministan Ayyuka da Gidaje kan kalaman da ya yi…

Jam’iyyar PDP ta yi amfani da hotonan wasu hanyoyi na kasar Laberiya, don maida martani ga Ministan Ayyuka da Gidaje kan kalaman da ya yi game da yanayin da hanyoyin kasar nan suke ciki.

A kwanakin baya, Fashola ya ce yanayin da hanyoyin kasar nan suke ciki, bai kai yadda ake kururutawa ba, inda ya ce wasu hanyoyin ma babu abin da ya same su. Wannan magana tasa ba ta yi wa wadansu jama’ar kasar nan dadi ba, inda wadansu suka zarge shi da boye ainihin munin halin da hanyoyin suke ciki.

Wani dan Majalisar Wakilai ya kalubalance shi cewa ya zaga hanyoyin kasar nan domin ganin irin halin munin da suke ciki na lalacewa.

Jam’iyyar PDP ta sa wasu hotuna a shafinta na Intanet, wadanda halin da suke ciki ya munana don nuna halin da wasu hanyoyin kasar nan suke ciki,

Jam’iyyar PDP ta kuma nemi Minista Fashola ya nemi gafara kuma ya sauka daga mukaminsa, saboda wannan jawabi nasa.

“Kowane dan Najeriya ya san irin halin da hanyoyin kasar nan suke ciki, inda suka kasance tarkon mutuwa, a cikin shekaru hudu da suka shige,” inji PDP.

Sai dai a wani bincike da kafar labarai ta Cable ta gudanar, ta gano cewa wadancan hanyoyi da PDP ta sanya hotunansu, ba na kasar nan ba ne, wasu hanyoyi ne a kasar Laberiya da aka buga labarinsu tun shekarar 2015.