Shugaban Jam’iyyar PRP ta Kasa, Malam Falalu Bello ya bayyana cewa jam’iyyar za yi bakin kokarinta wajen doke jam’iyyun APC da PDP a zaben shekarar 2023 mai zuwa.
Malam Falalu Bello ya ce sauran jam’iyyu ma ba za su samu galaba a kan Jam’iyar PRP ba domin PRP ta shirya tsaf wajen ganin ta taka gagarumar rawa a zabubbuka masu zuwa.
Malam Falalu Bello ya bayyana haka ne a wajen babban taron shugabannin jam’iyar na kasa da aka gudanar a Kaduna a ranar Asabar da ta gabata. “Zan so yin amfani da wannan dama in tabbatar wa ’yan uwana ’ya’yan Jam’iyyar PRP cewa an wuce zamanin damuwa da rashin tabbas a jam’iyyar. Domin jam’iyyarmu ta PRP a shirye take yanzu domin tunkarar kalubalen da ke gabanta.
“Mu da muke cikin wannan jirgi da zai yi wuya a tsayar da tafiyasa, akwai bukatar mu kara kaimi a tafiyar nan. Wadanda kuma ke waje har yanzu ya kamata tun wuri su shigo domin babu mai iya dakatar da mu a yanzu,” inji shi.
Malam Falalu Bello ya kuma ce an shirya taron ne domin a karbi sakamakon rahotannin kwamitocin da aka nada gab da zaben bara, domin duba matsaloli da kalubalen da ke fuskanta jam’iyyar a siyasar kasar nan da nufin yin gyara,” inji shi.
Kwamitocin sun mika sakamakon rahotanninsu lokacin taron ga shugabannin jam’iyyar.