✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyun siyasar da suke Gombe sun fi na Najeriya yawa – IPAC

Shugaban Gamayyar Jam’iyyun Siyasa (Inter Party Adbisory Council – IPAC) a Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Garba Sarkin Malaman Pantami ya bukaci Hukumar Zabe ta Kasa…

Shugaban Gamayyar Jam’iyyun Siyasa (Inter Party Adbisory Council – IPAC) a Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Garba Sarkin Malaman Pantami ya bukaci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta tantance sahihancin jam’iyyun siyasar da ake da su a jihar don gudun samun rudani.

Alhaji Muhammadu Garba, ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa da ke Gombe inda ya ce taron da gamayyar jam’iyyun siyasa suka gudanar a gidan gwamnati sun gano cewa yawan jam’iyyun da suke Gombe sun haura yawan wanda ake da su a kasa baki daya.

Ya ce a Najeriya ana da jam’iyyu 91 ne amma a Jihar Gombe sun gano cewa sun kai 97 don haka suke kira da Hukumar INEC ta fara tantancewa don a samu sahihin adadin jam’iyyun.

Sarkin Malaman Pantami, ya ce wani ba shugaban jam’iyya ba ne, sai ya je wajen masu kwamfuta su buga masa logon jam’iyya yana yawo yana cewa shi ne shugaban jam’iyya kaza.

Ya yi kira ga shugabanin jam’iyyun siysara da ke jihar su hada kai wajen ciyar da Jihar Gombe gaba tunda zabubbuka sun kammala kuma Allah Ya bai wa Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya na Jam’iyyar APC nasara, don haka a taru a mara masa baya don yana da kishin ciyar da jihar gaba.

Ya kuma bai wa Gwamna Inuwa Yahaya, shawarar cewa ya toshe kunnensa wajen nada kwamishinoni kada a kawo masa bara- gurbi don ya yi wa jam’iyya ko dan takara aiki lokacin yakin neman zabe, ya tsaya ya zabo wadanda yake ganin za su yi masa aiki irin yadda yake bukata ya nada su kwamishinoni da masu taimaka masa.

Ya yi kira ga matasa wadanda ya bayana da kashin bayan ci gaban al’umma kan su daina siyasar banga ana amfani da su ana ba su kudi wajen mayar da hannun agogo baya. Ya ce hakan ba daidai ba ne a taru a gina kasa da Jihar Gombe saboda ’ya’ya da jikoki masu tasowa nan gaba su mora.

Shugaban na IPAC ya yi kira ga al’ummar jihar kan su rika bai wa Gwamnan shawarwarin da suka dace kada su tsaya kawai su zuba masa ido saboda adawar siyasa.