Jamus da Jigawa za su hada hannu don tallafa wa manoma

Gwamnatin Jihar Jigawa ta shirya yin hadin gwiwa da kasar Jamus, domin bai wa manoma horo a kan yadda za su habaka aikin noma a jihar.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar manoma ta AFFAN, Malam Idris mai unguwa Jarda, a lokacin da ya halarci wani taron manoma shinkafa da aka yi a dakin taro da ke Dutse, fadar Gwamnatin Jihar Jigawa. Ya ce kungiyar mai suna CARI, za ta bai wa mata da maza manoma horon aikin noma irin na zamani a jihar, har mutun 25,000 a bangaran noman shinkafa da masara da dawa da gero da kankana da duk sauran kayan amfanin gona, da nufin habaka tattalin arzikin jama’ar jihar baki daya
Ya ce tuni ma ita wannan kungiya ta CARI da ta shigo jihar daga kasar Jamus, domin ba da wannaan gudunmawa ga manoman jihar, ta dauki nauyin bai wa mutane 15 masu shaidar digiri a bangaran aikin gona horo; domin fadakar da manoma da kananan malaman aikin gona, kan yadda za su fadakar da manoman yadda za su sarrafa shinkafa da sauran kayan amfanin gona, a lokacin da suke rainonsu.
Ya kara da cewa, su kuma wadannan mutane 15 da aka ba horon, an hada su da malaman gona 50 da za su ba su horo, a matakin kananan hukumomi, domin su kuma su sami damar shiga lunguna; su fadakar da manoma a karkara, don ganin shirin ya sami nasara. Ya ce tuni aka ware kimanin mutane 400 ana koyar da su dabarun aikin gona a yankin masarautar Hadeja, inda ta nan ne aka fara aiwatar da shirin a Jihar Jigawa. Kuma a kowane aji ana koyar da dalibai 30 tsawon kwanaki takwas. Daga nan kuma a tura wadanda aka ba horon gona kai tsaye, domin a fahimci cewa sun iya abin da aka koya masu a cikin aji.
daliban da aka koyar, ana ba su takardar shaidar samun nasara, inda kuma kungiyar ta CARI za ta ba kungiyoyin manoman da ta horar kayan aikin noma irin na zamani tare da tallafin kudi, domin kara wa manoman kwarin gwiwa; na ganin sun yi aikin noman kamar yadda suke da bukata. Haka kuma a ba su irin shukawa mai inganci da magunguna masu sanya irin habaka da sauri.
Ya kuma tabbatar da cewa shirin noman zai hade daukacin kananan hukumomin jihar 27 saboda ba wai noman shinkafa ba ne kawai, ya hada da sauran aikin gona kamar noman kankana da ridi da masara da gero da sauran kayan aikin gona. Ya ba da tabbacin cewa maimakon hasarar da manoman suke yi na wajan noma, za su yi dariya domin maimakon buhu 75 da manomin yake yi a cikin hekta daya, idan shirin ya dore, zai iya girbar shinkafa buhu 120 a cikin hekta daya kacal. Don    haka ya bukaci manoman jihar da su rungumi shirin noman shinkafar da ita kasar Jamus ta bullo da shi, da nufin agaza wa manoman; ta hanyar koya masu dabarun aikin gona irin na zamani.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya