✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jan hankali ga abokai a kan taimakon marayu

A rayuwar nan kana haduwa da mutane da yawa, a cikin su ne kuke iya shakuwa da wasu har ku kai ga zama aminan juna,…

A rayuwar nan kana haduwa da mutane da yawa, a cikin su ne kuke iya shakuwa da wasu har ku kai ga zama aminan juna, saboda haduwar zukatanku, har ya kai idan baka ga mutum ba kana iya zuwa neman sa don jin dalilin rashin ganinsa, kuma dan Adam yana son ya ga wanda ya damu da shi, saboda yana kyautata zaton bayan shi ba ba zai tagayyara ba.

Amma abin mamaki kuma abin takaici shi ne, wasu lokutan daga ranar da Allah Madaukakin Sarki ya karbi rayuwar mutum zuwa kwanaki arba’in a ma fi akasari su ne wadanda suka yi kokari masu zuwa ko kuwa su tambayi ya ya iyalan mamacin suke.

Abin sai ya yi kama da zumuncin daman don wata manufa ko zaman duniya kawai ake yi. Sau tari abokan da mutum ya yi zaman amana da su ba su cika  bibiyar halin da iyalan aminansa suke ciki ba. Hakika wasu na bukatar kulawa ta kowane bangare na al’umma kasancewar sun rasa wani babban jigo na rayuwarsu.

Lokuta da dama, aminai ko abokan arziki da aka zauna tare kan yi watsi ko biris da bukatun ’ya’yan aminansu kuma suna da halin kyautata musu.

Koda ba ka da halin daukar wasu daga cikin dauwainiyar yaran akwai bukatar bibiyar al’amuransu tunda matsayin uba kake gare su.

Kowanne dan Adam yana da iya kwanakin da Ubangiji ya rubuta masa game da iya zaman da zai yi a duniya, idan suka kare, sai ya koma ga Mahalliccinsa, kuma a saka wa kowace rai da abin da ta aikata. Kamar yaddda ya fada a cikin littafinsa Mai tsarki “ku ji tsoron ranar da za a dawo da ku wajen Ubangiji Ta’ala, sai kuma a saka wa kowace rai da abin da ta aikata, kuma ba wanda za a zalunta” (01:281).

Ta tabbata cewa mutum yana gyara lahirarsa ne tun daga nan duniya, ya kamata kuma mutane su kwana da sanin cewa yana da baya, shin idan Allah (SWT) Ya karbi rayuwarka, za ka so aminanka su yi biris da iyalan ka?

Ya ya za mu ji idan muka tsinci iyalanmu a irin halin da muka bar na wasunmu? Shin abin zai yi kyau kuwa? Ina koyarwar da Manzon tsira ya yi mana a kan rike marayu da kuma albishir da dimbin ladar da yake tattare da kula da marayu a cikin mu. Ya kamata mu duba da kyau mu gyara.

Ko ba a fada maka wannan ba, hankali da tunani ya isa ya sanar maka cewa wannan yaran ’ya ’yan aminina ne akwai bukatar na kula da su da kuma bincikar halin da suke ciki.

Daga Dauda Manu Mandau, Maiduguri (08065654274)