✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jan hankali ga kungiyoyin Izala da Shi’a (3)

Wannan tsokaci mai take na sama, an gabatar da shi a cikin shekarar 2014, shekara biyar ke nan cur da ta gabata. GIZAGO ya samo…

Wannan tsokaci mai take na sama, an gabatar da shi a cikin shekarar 2014, shekara biyar ke nan cur da ta gabata. GIZAGO ya samo shi ne daga turakar hazikin marubuci, MALAM AUWAL KANO (08064595353). Muhimmancin abubuwan da aka tattauna ya sa aka bijiro da shi, inda a makon jiya muka wallafa kashi na biyu na wannan tsokaci. A wannan karo ga kashi na uku kuma na karshe kamar haka:

A wannan karon, marubuci kuma mai tsokaci kan al’amuran yau da kullum, Malam Fatuhu Mustapha ne ya bude ta’alikin, inda ya ce: “Auwal, Allah Ya saka da alheri. Allah Ya sa wadanda aka yi domin su sun ji.”

Sai kuma Ahmad A. Daura Officer, da ya ga beken Auwal, inda ya ce masa: “Ka nakasa rubutunka da kanka da ka killace Kungiyar Izala da mabiya Shi’anci a matsayin matsalolin Musulmi a yau, a wannan kasa tamu Najeriya; bayan ga babbar matsalar da ta dabaibaye mu ta rikicin Boko Haram da ake asarar rayuka a kullum ta sanadiyyarsa, ban da talauci da gurbacewar ilmi da suka yi mana kaka-gida a cikin al’ummar Musulmi.

“Da irin wannan rubutu, da ma cewa ka yi ina ma a ce dukkan kungiyoyi irin su Kadiriyya, Tijjaniyya, Izala, Kala-Kato, Kura’aniyyun da ’yan Shi’a da sauransu, su hade kai a bi abin da ya zo a Alkur’ani Mai girma da karantarwar Manzon Allah (SAW) don a magance rarrabuwar kawunan da ake fama da ita, sanadiyyar bambancin akida da rubutun zai fi armashi kwarai.”

Shi kuwa Umar Abdussalam Daudawa, nasiha ya bijiro da ita cewa: “Kada dai garin neman gira a rasa ido, Auwal… Ba ni da burin fadar bakar magana ga kowa sai dai kowa na duniya in dai yana da’awar Musulunci, dole ne ya ji tsoron Allah a dukkan komai! Kai ka san kowace akida ce akidar Yahudawa. Don haka kalubale ne a gare ka, in dai har ba za ka fito fili ka fadi gaskiyar me ka sani ba, to dole ka yi shiru (wannan shi ne mafi raunin imani). Zai fi maka alheri, da ka yada wasi-wasi cikin zukatan mutane! Auwal, ba dole ba ne sai ka yi magana kan akida za ka yi suna ba! A’a, tun kana rubutun tatsunniyoyi muka san ka kuma ka yi suna. Sai ka gode wa Allah kan hakan, amma dai wallahi sai ka ji tsoron duk lokacin da za ka yi magana kan akida, domin kuwa akida ita ce mutum, ita ce imani, ita ce Musuluncin ma gaba daya. Don haka a ji tsoron Allah!”

Sai kuma Yusif Umar Baba, ya fadi nasa ra’ayin cewa: “Addinin Shi’a daban, addinin Musulunci daban, ba za mu yarda ’yan Shi’a su rika shiga rigar Musulmi suna bata mana suna ba. Don haka dole mu fafata don ba mu da alaka da su, bare mu hada kai tsakanin gaskiya da karya.”

Sai kuma Al-Mustapha Adam Muhammad da ya shiga kare Auwal ya yi da cewa: “Mene ne kuskuren Auwal? Kodayake na lura ’yan Shi’a ke ganin beken rubutunsa. Shin marubuci ba ya da damar shiga kowane bigire ke nan? Haba ’yan uwa! Ku kara bitar abin da ya rubuta.”

Umar S. Ahmad kuwa ya ce: “A sanina da alkalamin Auwal, gwauron alkalami ne. Ba ya kasa rubutu a dukkan fannoni, wanda in ban manta ba ma ya taba yin rubutu a kan wannan gaba da ka kawo kuma abin da na lura da shi, shi ne, ba a cewa yi rubutu a kan abu kaza ka ce kaza; sai dai ya yi rubutu a kan abin da ransa ya ga dama, zuciyarsa ta aminta. In dai Auwal ne, wata rana ma a kanka ma sai ka ga ya yi rubutu da irin kayan da kake sakawa tare da abincin da kake ci zuwa muhalli.”

Janare Bature kuwa shawara ya ba Auwal, cewa: “Ni kam nike da ta cewa. Allah Ya saka da alheri Auwal amma ina so kowane bangare ka kasance mai adalci a rubutunka.”

Sannan ya sake dawowa da kariya ga Auwal, yana cewa: “Umar Abdussalam Daudawa, ba neman suna ya fito ya yi ba, magana ce ta gaskiya. Idan kaifin alkalaminsa ya biyo, to kowane ne zai fede masa gaskiya har wutsiya. Ba ya neman suna kuma ba shi yake da bukata ba, ehe; sai ka gyara kalamanka.”Ahmad A. Daura: “Marubuci dama ba a bukatar ya zama marar ra’ayin kansa, sai dai a wannan rubutu na yau, Auwal na nuna kamar bai yi cikakken bincike ba kafin ya yi shi, dubi yadda yake bayyana cewa: “har yau na kasa gane wa ke da gaskiya tsakanin Izala da ’yan Shi’a.”

Abdullahi Sani Malumfashi ya goyi bayan Auwal da cewa: “Maganar Auwal haka take, Allah Ya ganar da mu gaskiya, Ya ba mu ikon bin ta.”

El-Ameen Daurawa kuwa ya ce: “Mu dai ’yan fahimta fuska ne, duk wanda ya zo da gaskiya mu bi shi, idan ka zo da sabanin haka mu kyale ka da abinka.”

Elbashir Lawan kuwa jawo hankali ya yi ga marubucin, inda ya gaya masa cewa: “Malam Auwal, muna jira mu ji matsalar ’yan Darika, sai mu hada mu ware wadanda suke a kan tafarki na gaskiya. Lura ga yadda ’yan Darika suke bautar shaihunnansu. Kuma muka ji wani mawaki na ’yan Darika yana fadi a cikin wakensa, ‘Inyass bai haifa ba, ba a haife shi ba.’ Ya kara da fadin, ‘Shehi shi ya halicce shi…’ Amma abin takaici sai muka ga malaman Darika suna goyon bayansa. Amma muna jira mu ji abin da Malam Auwal zai ce a kansu, su ’yan Darikar; musamman ma irina ’yan ba-ruwanmu da ba mu daga cikin wata kungiya Izala, Shi’a ko Darika. Idan aka yi mana bayani, watakila mu samu gurbi a daya daga cikinsu.”

Ita kuwa marubuciya Sa’adatu Baba Ahmad, goyon baya ta yi ga marubucin, inda ta ce: “Wallahi su ne, Auwal; na jinjina maka da wannan rubutu.”

Sai kuma ta’alikin Muhammad Abubakar: “Gaskiya babu alakar Sunnah da Shi’a ta kusa ko ta nesa, domin tuni na fahimci cewa Shi’a ba su tare da al’ummar Musulmi. Za ka fahimci haka ta hanyar littattafansu, maganganunsu da dabi’arsu kai hatta a Kalumatu Shahada, Shi’a suna yi mata gyara.”

Daga nan kuma sai ta’alikin Muhammad Bello, wanda ya ce: “Auwal, na yi matukar ta’ajibin wannan rubutu matukar gaske, a ce kai ka yi wannan rubutu; inda kai- tsaye rubutun an yi shi ne a kanmu ’yan Shi’a, mabiya Malam Zakzakiy (h). Domin inda alkalaminka ya nuna ke nan, wanda inda za ka yi adalcin da kwararrun marubuta da suke da ’yancin tunani, wanda su ba su da bangaranci ko ta’assubanci da sai ka yi bincike a tsakanin kowane bangare. Misalin mu Shi’a, muna da malamai da suke da mabiya masu yawa a kasar nan da sai ka tuntube su; wane irin aiki suke yi na ganin an samu ci gaba a da’irar Musulunci? Domin akwai abubuwa da yawa da ’yan Shi’a ke yi kuma ko yanzu mun ga wadanda suka nuna kansu don rubutun ya ba su damar cin mutunci ga Shi’a, domin duk ga su nan suna batanci gare mu kuma dama manufar rubutun a fili take. Ga shi nan ’yar manuniya ta nuna abin da ake fada wa ’yan Shi’a daga farkon rubutunka. Lallai kai kam ta janibinka, ciniki ya fada. Ka yi rubutu amma wani bangare ya samu damar cin mutuncin daya bangaren, har yana fidda su daga cikin Musulunci. Humm! Da ma za ka yi koyi da marubutan adabin Hausa, irin su Farfesa Ibrahim Malumfashi, Farfesa Yusuf Adamu, Malam Ibrahim Sheme da Ado Ahmad Gidan Dabino da Malam Nasir G. Ahmad, duk suna cikin wannan kafar ta Facebook amma sun kauce wa rubutu kan akida.”

Bari kuma daga karshe mu rufe wannan takaddama da ta’alikin Muhammad Abubakar, wanda ya shaida wa Muhammad Bello cewa: “Ai marubuci na da damar yin rubutu a kan komai, amma abin da ya fi dacewa da shi, ya fahimci abu kafin ya yi rubutu a kai. Amma Auwal bai fahimci mene ne Izala ba, har yake hada ta da Shi’a a ma’auni guda.”

Mun kammala