✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Japanawa na murnar samun daukar nauyin gasar Olamfik ta 2020

Mutanen Japan musamman wadanda ke zaune a babban birnin kasar watau Tokyo sun barke da murna jim kadan bayan Kwamitin da ke kula da shirya…

Firaministan Japan Shinzo AbeMutanen Japan musamman wadanda ke zaune a babban birnin kasar watau Tokyo sun barke da murna jim kadan bayan Kwamitin da ke kula da shirya wasannin Olamfik (IOC) ya bayyana kasar a matsayin wacce za ta dauki nauyin gasar a shekarar 2020.
A karshen makon jiya ne dai kwamitin ya zabi kasar daga cikin kasashe uku da suka fafata wajen neman daukar nauyin wasannin. kasashe biyu da suka fafata da Japan sun hada da birnin Madrid da ke Sifen da kuma na Istanbul da ke Turkiyya.
Da wannan dama da ta samu, Japan za ta dauki nauyin gasar sau biyu kenan a tarihin gasar.
Jim kadan da bayyana kasar a matsayin wacce za ta dauki nauyin gasar ne sai al’ummar kasar suka kwarara kan tituna dauke da tutocin kasar da kuma na shugaban kasarsu suna murna ta hanyar yin kade-kade da raye-raye inda suka shafe daukacin daren don murna.
Rahotanni sun ce an ga gidan otal-otal da na dakunan cin abinci da wuraren shakatawa cike da jama’a har zuwa wayewar gari don murna.
Kwamitin shirya gasar Olamfik ne ya amince da zabar Japan a matsayin kasar da za ta dauki nauyin gasar bayan daukacin ’yan kwamitin sun kada kuri’arsu a kanta.
Sai dai masana harkar wasanni suna shakku ko kasar za ta iya daukar nauyin gasar musamman ganin yadda take fama da matsalar kwararar tuturin zafi daga nau’urorin nukiliyarta. An ce wannan matsala ta sa yanayin zafin kasar ya wuce kima inda kasar mafi yawan baki masu zuwa don yin kasuwanci da ’yan yawon bude ido suka ragu matuka a ’yan kwanakin nan.
Tuni Firaministan kasar Shinzo Abe ya bayar da tabbacin kasar za ta shawo kan al’amarin kafin a fara gasar kuma ya ce tuni ya ware Dala miliyan 470 kwatankwacin Fam miliyan 300 don shawo kan al’amarin.